MILIYOYIN HAUSAWA NA GUDANAR DA BIKIN RANAR HAUSAWA TA DUNIYA



Kamar kowacce shekara al'ummar Hausawa na amfani da kowacce 26 ga watan Agusta don gudanar da bikin ranar Hausa ta Duniya, ranar da bisa al'ada kamar yadda aka faro ake amfani da ita wajen shagulgulan nuna al'adun kabilar ta Hausawa
wadda ke ci gaba da yaduwa a sassa daban-daban na Duniya.


Kamar kowacce shekara a bana ma, bikin wannan rana na gudana a kasashe daban-daban musamman a tushen harshen cikin yankunan da suka kunshi arewacin Najeriya da kuma kudancin Jamhuriyyar Nijar. 


Masana na sanya harshen na Hausa a sahun harsuna masu saurin yaduwa inda a yanzu haka ake da miliyoyin masu amfani da shi, da alkaluman da aka tattara cikin shekarar 2017 ke nuna cewa akwai fiye da mutane miliyan 86 da dubu dari 8 da 4 da ke amfani da shi ko dai a matsayin harshen farko ko kuma na biyu a kasashe daban daban na
yammacin Afrika ciki har da Benin da Kamaru da Ivory Coast da Chadi baya ga Sudan da Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya.


Kamar yadda alkaluman na 2017 suka nuna harshen na hausa na matsayin harshe na biyu mafi girma kuma wanda
aka fi amfani da shi a nahiyar Afrika, yayinda ya bazu zuwa wasu nahiyoyi ciki har da Asiya da uwa uba Turai da
Amurka.


Alkaluman na 2017 sun nuna cewa cikin kasashen da Hausa ta fantsama tare da samun gindin zama a Afrika, Ivory Coast ce kan gaba a yawan masu amfani da harshen na hausa da jumullar mutum dubu 835, sai Sudan da mutum
dubu 700 kana Kamaru da mutum dubu 400. Sauran sun hada da Chadi mai mutane dubu 287 da ke amfani da harshen Hausa kana Ghana da mutane dubu 281 sannan Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya da mutane dubu 33 Eritrea da mutane dubu 30 kana Benin dubu 36 da 360 sai Equatorial Guine amai mutane dubu 26 akwai Gabon da mutane dubu 12 kana Algeria mutane 11 sannan gambiadubu 10.


Ana dai gudanar da bikin wannan rana tamkar Sallah a wasukasashe musamman tsakanin al'ummar ta Hausawa mazauna wasu nahiyoyi irin Turai da kan shirya gangami na
musamman.

                      Mnnu//Ng0027

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post