WANI BABBAN SHEHIN MALAMIN SUNNAH YA RABA BUHUNAN SHINKAFA KYAUTA DON TAIMAKA WA AL'UMMA A JIHAR BAUCHI


 WANI BABBAN SHEHIN MALAMIN SUNNAH YA RABA BUHUNAN SHINKAFA KYAUTA DON TAIMAKA WA AL'UMMA A JIHAR BAUCHI....!!l

A ranar Alhamis 17-08-2023 ne Babban Malamin Ahlu Sunnah a jihar Bauchi Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya raba kyautar shinkafa Buhu dubu daya a kofar gidansa dake Dutsen Tanshi Bauchi wa mabukata kyauta Kuma ba wannan karon bane Malam ya saba irin wannan kyauta domin ya kyautatawa mabukata dake unguwarsa a BauchivMalam Ahmad Tijjani Guruntum dan kasuwa ne, ba dan siyasa bane, baya karban kudin 'yan siyasa ya musu talle, amma ku dubi yadda yake taimakon jama'a da dukiyarsa

Na tabbata Wallahi akwai Malaman da sun ninkashi a dukiya, akwai 'yan siyasa da sun ninkashi a dukiya amma basuyi irin abinda yake yi ba wajen taimakon al'ummah, duniya kawai suka sa a gaba A wannan yanayin da muke ciki Wallahi akwai mabukata, 'yan uwa Musulmi suna kwana da yunwa suna bukatar a taimakesu, tabbas da Malamai masu arziki musamman wadanda suke karban kudi a gurin 'yan siyasa zasu ware wani abu daga dukiyarsu su taimaki mabiyansu kamar wannan to da an samu sauki Amma abin takaici zakaga babu abinda irin wadannan Malamai 'yan siyasa sukeyi sai gina kamfanoni da gidajen alfarma da auri saki, don haka ba daidai bane ku karbi kudi a gurin azzaluman 'yan siyasa ku yaudari mabiyanku kusa su zabesu sannan ku kasa tallafa musu daga abinda kuka karba

Muna rokon Allah Ya yalwata dukiyar Malam Ahmad Tijjani Ya saka masa da Alkairi 🙏🏼

Real Naseer Umar Alhassan 0015

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post