Cewar Sheikh Ibraheem El,Zakzaky (H),Yanzu an shigo mana da abin da ba mu san mene ne ba, kowa in ka tambaya mene ne mafita? Saboda Allah meye mafita? Kuma na ga abin na ta kara tabarbarewa ne, sha’anin tsaron nan da ake ta surutu kullum yana dada tabarbarewa ne, kowa yana cikin zaman dar-dar. To mene ne magani?”


Abin da muke gani shine bamu da mafita sai a wajen Allah Ta’ala, kawai yanzu mu dukufa da addu’o’i ne. Domin batun cewa ka kare kanka, idan da ace yan fashi ne ke zuwa fashi da makami in suka ji an yi harbi za su gudu. 


To amma wadannan mutanen suna zuwa da irin bindigogin soja ne, shi yasa muka tabbatar da wadannan mutanen tirenin ake musu, kuma bindigogin ba irin wadanda ake sayarwa a kasuwa bane.


Ko lokacin da suka kai hari gidan yarin Kuje, sun yi amfani da nau’in bindigogi uku wadanda ba wacce ake sai da irinta a kasuwa. Sun yi amfani da RPG wanda ake harbin tankards da shi, irin bindigar da akan goya a kafada tana da baki biyu, in harsashi ya fito wuta zai fita ta baya, don haka ba a tsayawa a bayanta, da ita suka harbi ‘gate’ din gidan yarin. 


A yaki ake amfani da ita wajen harbin tankan yaki, don in RPG ya fita yana kutsa cikin karfe, sai ya shiga cikin karfe sannan yake fashewa, to amma wadannan wai suna da shi.


“Sannan kuma akwai wata nau’in bindiga da ake ce mata AA, wacce take harba manya-manyan harsasai. Sannan banda wannan kuma da A.K mai jigida din nan, wacce take sarrafa kanta, tana diban harsasai, da irinsu suka je, sai su goya a kan mota su yi ta harbi. To don Allah, idan za ka samu bindigarka yar karama ka sa a aljihu, ina kai ina iya ma wadannan? To amma dai ba za su fi karfin Allah ba, Allah mai iko ne a kan komai.


Makamai ne irin na sojoji (wadanda ake kira mahara suke amfani da su), da su suke zuwa su dira su tarwatsa gari, manufar shine kawai a saka mutane a cikin halin rashin kwanciyar hankali,


Ma'asumah Nigerian News Update

              Mnnu//Ng0027

2023-08-18 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post