Ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya sun soki matakin gwamnatin tarayya na bayar da naira biliyan 180 ga jihohi


Ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya sun soki matakin
gwamnatin tarayya na bayar da naira biliyan 180 ga
jihohi domin raba wa jama'a a matsayin rage
raɗaɗin cire tallafin mai.
Haɗakar ƙungiyoyin ƙwadagon NLC da TUC ta ce a
yanayin yadda al'amura ke tafiya a Najeriya, ‘yan
siyasa ne za su ci gajiyar tallafin na naira biliyan
biyar da za a bai wa kowacce jiha, amma ba
talakawan da aka fitar da kuɗaɗen domin su ba.
A ranar Alhamis ne, gwamnan jihar Borno Babagana
Zulum ya sanar da shirin gwamnatin na bai wa
kowacce jiha naira biliyan biyar da tirelolin shinkafa
180 domin rage wa jama’a zafin cire tallafin.
Matakin ya zo ne bayan wani taron Majalisar
Tattalin Arziƙin Ƙasa, a ƙarƙashin jagorancin
mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima a
Abuja.
Gwamnan na Borno ya ce, jihohin za su yi amfani
da naira biliyan biyar ɗin ne domin sayen buhunan
shinkafa 100,000 da masara da kuma takin zamani,
waɗanda za a raba ga talakawa.
Zulum ya ce bisa la’akari da halin da ake ciki da
kuma ƙudurin gwamnati na shawo kan tashin
gwauron zabi da farashin kayan abinci ke yi ya sa
gwamnatin tarayyar a makon da ya gabata ma ta
bayar da tirelolin shinkafa biyar-biyar ga kowacce
jiha a ƙasar.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa dukkan matakai da
gwamnatin ta ɓullo da su saboda janye tallafin man
fetur, ba su samu karɓuwa ba wajen ƙungiyoyin
ƙwadago na ƙasar, domin tun da farko sun ba da
sharaɗin cewa gwamnati ta gyara matatun mai na
cikin gida, kafin janye tallafin.

Real Naseer Umar Alhassan 0015

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post