RAYUWAR NAN TANA DA BAN TSORO 😭


 RAYUWAR NAN TANA DA BAN TSORO 😭

Mai gidan ya koreshi tare da iyalansa saboda ya kasa biyan kudin hayar gidan sa, sannan ya nemi lamuni daga manajan kamfanin da yake aiki da shi Saboda Ya samu Kudin hayan, amma bai samu ba. Ya tuntubi mai fada a ji a yankinsa, amma ya kasa samun taimako. Sannan ya kira yan uwansa a waya amma babu wanda ya taimaka masa ya shiga facebook yayi posting yana neman agaji amma abinda ya samu shine 2likes kacal and 0 comments. Abin yayi masa katuro sai ya aika wa abokansa sakwanni 120 da ke cikin jerin sunayensa, yana neman su tallafa musu Naira 100,000. Abin takaici, mutane 10 ne kawai suka amsa sakon sa sanna Shida a cikin 10 din sun ce babu abin da za su bayar.

 Mutum daya ne cikin mutum 4 ya ba shi Naira 20,000, amma sauran suka ci gaba da ba shi hakuri, daga karshe kuma ya daina daukar wayarsa Abun yakai har Mai gidan ya kulle gidan! Aka jefar kayayyaakin su Sannan iyalansa aka barsu a kofar gidan da kayan nasu a tsaye, sai yasakr zaga ko'ina yana neman taimako amma bai samu ba sai can dare Yafito ci gaba Da Neman mafita, yana cikin neman mafitan, sai wata babbar mota ta bigeshi ta kashe shi nan take. shi har lahira , Kuma wai Nan take mai gidan ya ruga ya bude kofa domin 'yan uwansa su shiga domin tarbar makokin rasuwarsa 

Mutumin mai fada a ji wanda tun da farko ya ki taimaka masa, ya dauki wasu kayan abinci da kayan masarufi ya kai wa 'yan uwa saboda ayi girki ba yan zaman makoki. Daga baya aka fara shirye-shiryen binne shi, kuma abokansa, wadanda sukaki Taimakon sa suka kafa kwamitin gidauniyan tara Naira miliyan 1,200,000 ta hanyar bayar da gudunmawa don ciyar da masu gaisuwa da zasu zo daga wurare daban-daban. Haka kuma abokan aikinsa suka tara Naira 300,000 domin karbar rumfuna, kujeru da sauran kayayyaki. Jama'a me yasa bama kula da damuwan mutane sai lokacin da suka rasu....? Ya Allah ka cigaba da hadamu da mutanen Kirki.

Ku Danna Kuyi Following👉 Asperger

Real Naseer Umar Alhassan 0015

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post