Da Dumi Dumi In ji Hajiya Naja'atu Bala Muhammad Cire tallafin Man Fetur tsantsar Zalunci ne Dama na faɗawa Yan Nigeria Kada Su Zabi Bola Tunibu


 DA DUMI DUMINSA: Cire tallafin Man Fetur tsantsar Zalunci ne Dama na faɗawa Yan Nigeria Kada Su Zabi Bola Tunibu Babu Abinda Zai yiwa Arewa Amma Sabida Mafi Yawan Mutanen Arewa Munafukai Ne Kuma Makwadaita, In ji Hajiya Naja'atu Bala Muhammad

Fitacciya kuma gogaggiyar ‘yar siyasarnan, Hajiya Naja’atu Muhammad ta caccaki gwamnatin Shugaba Bola Tunibu inda ta ce tabbas gwamnatin ta ba su kunya kuma a baibai gwamnatin take tafiya. Sannan ta bayyana ‘yan arewa a matsayin munafukai kuma matsorata kuma makwadaita. Ta bayyana hakan ne a yayin hirarta da gidan Rediyon RFI Hausa. Wakilin Madogara TV ya rubuta muku cikakken hirar da aka yi da ita. Ga hirar na ta ne kamar yadda yake: “Dokar farko a tsarin mulkinmu shi ne kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Gwamnati a duk duniya ma babban aikinta shi ne wannan. Idan wannan gwamnatin (kowacce gwamnati ce) ta kasa kare rayuka da dukiyoyin al’umma, ba gwamnatin ba hukuma, ba ta da amfani.”.  

“Saboda haka wannan gwamnatin ba ta yi wa al’umma amfanin komai ba don ta kasa kare musu dukiyoyinsu da rayukansu”. 

Hajiya Naja’atu ta ci gaba da cewa; “ba a rasa (masu fada mata gaskiya ba), ko mu muna fada. Yanzu ma fada muke, amma mafi yawa musamman mutanen arewa, shiyasa ran mutumin arewa ya zama ba shi da amfani. Mafi yawan mutanen Arewa munafukai ne, mafi yawansu matsorata ne, mafi yawansu makwadaita ne! Ka gani da shugabanninsu da Sarakunansu mafi yawa, da Malamansu mafi yawa wadanda da sune aka dogara da ma’aikata da ‘yan siyasarsu. ‘Yan siyasarsu banda tumasanci da karya da sata ba sa komai. Sun shiga siyasa ne ba don al’umma ba sai don su cika aljihunsu. Ana kashe ‘yan arewa kamai kiyashi. Banda a arewa ba inda za a yi wannan a zauna lafiya”. Mutane da yawa suna kallon Malamanmu a matsayin shugabanni, amma yanzu ka ga wannan ta kau. Malamai aikinsu idan siyasa ta zo, shi ke nan a ba su su je su yi babatu su ce a zabi wanda dai ya ba su kudi, babu Allah a gabansu. Shiyasa za ka ga da a ce mutum yana kuka an karkashe musulmi

Real Naseer Umar Alhassan 0015

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post