Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un


 A Tauhidin Musulmin Arewa ko nace Bahaushe, mutumin nan da ya rataye kansa saboda matsi da kuncin rayuwa, bayan Maluman da yai Imani da su sunce masa Haramun ne Zanga Zangar naiman yanci a wurin Shugaban da ka bashi kuri'a kukai yarjejeniyar zai maka Adalci, zai ba ka aikin yi, zai gina maka gobenka zai samar maka da tsaro. Wadda a karkashin wannan dokar ta dimokradiyyar Nijeriya, haƙkin ka ne kai Zanga zangar lumana don naiman yancin ka da ka rasa, ko wata bukata da ba'a biya maka ba. Da zaije yai sata, yan uwansa Musulmi Hausawa ne zasu lakada masa dukan tsiya in yai rashin sa'a aka kama shi, ba mamaki yana da Iyalai, cikin masu Kuɗin mu zai wahala a samu wani wadda zai bashi jari don gina kasuwancin da zai dauki nauyin Iyalansa da al'amuran su na yau da kullum.

Da zaiyi bara, zai wahala ake bashi abin Sadaka, tare da cewa yanzu masu Arzikin basu cika fidda zakkah yadda yakamata ba, ba wadda ya dubi halinda yake ciki, amma daga ƙarshe mutanen mu Hausawa ne za jisu suna cewa, "Ya kashe kansa a banza, kuma ɗan wuta ne shi". Wato Kotun Allah da za'a tsaida ta ranar lahira, in irin wacce Musulmin Bahaushe ne ke sauwalawa a kwakwalwar sa, ba shakka da Azzalumai sunci banza. Muna roƙon Allah ta'ala ya jikan wannan mamaci da ya rataye kansa saboda kuncin rayuwa, ya karɓi uzurinsa ya yafe kurakuransa, ya tsinewa wadannan miyagun Azzaluman, Allah ka nuna mana ranar da Talakawa za suyi fito na fito da wannan tsinannan tsarin da ya zuke mutane, mutum da hankalin sa ya zama kamar mahaukaci saboda yanayin rayuwar da aka jefa mu cikinta da gangan da ganganci.

Muhd Bala Afuwa

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post