Mu yanshi'a bamu goyon bayan Anfani da karfin soja Ga yan'uwanmu musulmai na Nijar-


 Mu yanshi'a bamu goyon bayan Anfani da karfin soja Ga yan'uwanmu musulmai na Nijar.

-
Bisa dalili kamar haka.:
-
1) Kaso 99 cikin dari na mutanan nijar musulmaine, Musulumci ya haramta zubar da jinin musulmi bada laifin komai ba. Shi kuma farmakin da akace za'a kaimasu ba kare addini bane. Kare tsarin kafurci ne, wanda ba na Allah ba. Wato dimukradiyya. Bamu goyan bayan atura wadanda ba musulmaiba su kashe musulmi, hakan zai iya jawo rikicin addini.
-
2) Idan Aka kashe yan Nijar, to yan uwan mu aka kashe, domin auratayya ta hadamu dasu, wadda takaiga munzama abu guda. Al'adunmu guda dasu. Ga kuma yare ya hadamu, gakuma hakkin makwabtaka. Kuma Yan najeriya yan arewa sune za'a raunata, domin akwai kasuwanci mai karfi atsakanin mu, hakan zai haifar da yan gudun hijira masu yawa.
-
3) Idan najeriya tanada karfin kai hari a nijar to sojojin akaisu su yaki yan ta'adda da kullum suke kashemu ba dare babu rana. Saboda mi kunada karfin yakar wata kasa, amma cikin kasarku baku iya komai.
-
4) Nijar da yan nijar sunada Hakkin su zabi tsarin da suke so surayu akansa. Duk da tsarin da ya dace dasu shine Musulumci, saboda kusan duka kasar musulmai ne. Abinda kawai suke bukata shine su zauna, su hada kansu guri daya suyi tsarin musulumci. Amma tilasta masu tsarin dimukradiyya zalunci ne.
-
5) Kasar nijar Ta yan nijarce, sukeda hakkin suzabi kasar da zasuyi mu'amala da ita, idan sun kori faransa da america sun kawo Rasha, wanna zabin nasu ne. Bai kamata wani yace dole sai sunyi Alaka da wata kasa ba. Yin hakan tauye hakkin dan adam ne.
-
Ya kamata najeriya ta maida hankali akan matsalolin da take fama dasu, ba wai ta jawo wata matsalar ba. America da faransa sunaso suyi anfani da najeriya domin gyara miyarsu, mukuma su barmu cikin matsala. Kuma ko ankai harin ba nasara za'a samuba sai Al'amarin ya kara lalacewa.
-
Khadim Arkam A/Hadi. Abu Ashtar .
Real Naseer Umar Alhassan 0015

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post