YADDA AKE JONA SALLAH BAYAN LIMAN

 

YADDA AKE JONA SALLAH BAYAN LIMAN


Dai dai da fatawoyin sayyid khamnei(Q's)


Ya halasta mutum ya jona sallah bayan liman a kowace Raka'a yake, in dai bai kai ga tasowa daga ruku'u ba. Idan kuma an iske ya dago, sai a jira Raka'a ta gaba a jona. 


Kowace Raka'a tanada hukuncin ta.

Raka'a ta daya (1)

Idan mutum ya riski liman a Raka'a ta farkon sallah, toh an dauke mashi karatun sura da fatiha na sallar duka, amma zai yi sauran azkar da kuma sauran ayyukan da ke cikin sallar.


Raka'a ta biyu (2)

Idan mutum ya samu liman a Raka'a ta biyu, shima ba zaiyi karatu ba, amma zaiyi kunuti da ruku'u da sujuda a tare da liman, idan anzo zaman tashahhud kuma sai ya yunkura har sai liman ya gama, idan sallar mai rakaa biyu ce sai ya tashi ya kawo ta biyu ya kammala, idan kuma mai ukku ce ko hudu, sai ya kawo fatiha da sura a lokacin da liman ke fatiha ko azkar na Raka'a ta ukku, sannan ya wajaba gareshi yayi tashahhud a lokacin da liman ya mike zai kawo Raka'a ta hudu, sannan ya tashi yabi liman a ta hudu shi kuma yana ta ukku. A Raka'a ta karshe kuma, sadda liman zai yi tashahhud ya sallame shi kuma sai ya tashi yayi ta karshe ya sallame sallarsa.


Raka'a ta ukku da hudu na zuwa inshallah don gujewa dogon rubutu.

Real Naseer Umar Alhassan 0015

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post