An Kwashi Yaran Dake Fama Da Cutar Yunwa Wacce ta kusa Sanadiyar mutuwarsu A Katsina


 An Kwashi Yaran Dake Fama Da Cutar Yunwa Wacce ta kusa Sanadiyar mutuwarsu A Katsina Zuwa Yanzu Suna Asibiti Domin Duba Lafiyarsu Sannan An Siya musu kayan Abincin Mutane da dama sun kirawo ni akan neman sanin haƙiƙanin halinda waɗannan bayin Allah suke ciki gaskiya Alhamdulillah tun bayan da Ɗan Uwa Ahmad Bilhaqqi da abokanin shi suka ziyarci waɗannan bayin Allah tare da fitar da Bidiyon nan dake ta yawo an samu Mutane daga wurare daban-daban suna kira tare da taimakawa. Alhamdulillah an kai yaran Asibitin Turai domin duba lafiyar su inda kuma Alhamdulillah lafiya ƙalau suke illa dai yunwa da ta tagayyara su, ita kuma Mahaifiyar tasu an kai ta Asibitin koyarwa dake nan Katsina Wanda Hon. Sani Aliyu Danlami yace ya ɗauki nauyin kulawa da ita, Allah yasa ka mashi da Alkhairi Amin.

Ƴan uwa suna ta taimakawa bakin gwargwadon iyawar su mai dari mai kobo, gaskiya Alhamdulillah babu abinda za a ce sai godiya ga Allah. Ga masu tambayar ko an tabbatar da Mijinta yana raye ko lafiya, tabbas an tabbatar da cewa yana raye kuma lafiyar shi ƙalau kawai dai ya gudu ya bar su ne saboda yanayin rayuwa, yanzu haka ana ƙoƙarin sanin taka maimai inda yake domin a san abinda ya kamata a yi da yaddar Allah. Muna godiya ƙwarai da gaske ga dukkanin Al'umma da suke taimakawa kamar yadda za'a gani ga Buhun Dawa nan da na Masara kai harma akwai na Shinkafa da sauran kayan masaruhi Allah yasa ka ma kowa da Alkhairi Amin.


Bashir Yar'adua

Real Naseer Umar Alhassan 0015

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post