RUDANIN DA MUSLIMCI DA MUSULMAI SUKA FADA CIKI !!!

 @ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED  @


TA INA ZA MU SAN SUNNAR ANNABI (S. A. W. W) HAR MUYI RIQO DA ITA  ?


Ko da ba za ka fahinceni a farko ba, amma in har kayi haqurin bin wannan rubutu zuwa qarshe za ka fahinci tabbas akwai rudani cikin muslimci wanda wasu su kayi sanadin kasancewarsa haka. Wannan rudani da ake cikinsa kuwa matuqar aka qare rayuwa a kansa tabbas akwai alamar tambaya wajen shiga Aljannar mutum. 


Annabi Muhammad (S. A. W. W) shine Annabin qarshe wanda Allah ya tayar kuma ya sanya shi a matsayin mai shiryarwa wanda za a shiryu ta hanyar koyarwarsa. Wannan dalili yasa kafin barinsa duniya yayi mana gargadi  wajen bin sunnarsa da ta Halifofinsa don kaucewa fadawa cikin rudani wanda a halin yanzu haka ake ciki.


Imam Nawawi da Abu Dawud da Tirmidhi sun riwaito wannan hadisi kamar haka :


๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ


157» ุงู„ุซุงู†ูŠ: ุนู† ุฃَุจูŠ ู†َุฌูŠุญٍ ุงู„ุนِุฑุจุงุถِ ุจู†ِ ุณَุงุฑูŠุฉ ุฑุถูŠ ุงู„ู„ู‡ ุนู†ู‡ ู‚َุงู„َ: ูˆَุนَุธَู†َุง ุฑุณูˆู„ُ ุงู„ู„ู‡ِ ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู… ู…َูˆุนุธุฉً ุจَู„ูŠุบَุฉً ูˆَุฌِู„َุชْ ู…ِู†ْู‡َุง ุงู„ู‚ُู„ُูˆุจُ، ูˆَุฐَุฑَูَุชْ ู…ِู†ْู‡َุง ุงู„ุนُูŠُูˆู†ُ، ูَู‚ُู„ْู†َุง: ูŠَุง ุฑุณูˆู„َ ุงู„ู„ู‡ِ، ูƒَุฃَู†َّู‡َุง ู…َูˆْุนِุธَุฉُ ู…ُูˆَุฏِّุนٍ ูَุฃูˆْุตِู†َุง، ู‚َุงู„َ: ((ุฃُูˆุตِูŠูƒُู…ْ ุจِุชَู‚ْูˆَู‰ ุงู„ู„ู‡ِ، ูˆَุงู„ุณَّู…ْุนِ ูˆَุงู„ุทَّุงุนَุฉِ ูˆَุฅู†ْ ุชَุฃู…َّุฑ ุนَู„َูŠْูƒُู…ْ ุนَุจْุฏٌ ุญَุจَุดِูŠٌّ، ูˆَุฅِู†َّู‡ُ ู…َู†ْ ูŠَุนِุดْ ู…ِู†ْูƒُู…ْ ูَุณَูŠَุฑَู‰ ุงุฎุชِู„ุงูًุง ูƒَุซูŠุฑًุง، ูَุนَู„ูŠْูƒُู…ْ ุจุณُู†َّุชِูŠ ูˆุณُู†َّุฉِ ุงู„ุฎُู„َูุงุกِ ุงู„ุฑَّุงุดِุฏِูŠู†َ ุงู„ู…َู‡ْุฏِูŠِูŠِّู†َ ุนَุถُّูˆุง ุนَู„َูŠْู‡َุง ุจุงู„ู†َّูˆุงุฌِุฐِ، ูˆَุฅِูŠَّุงูƒُู…ْ ูˆَู…ُุญْุฏَุซَุงุชِ ุงู„ุฃُู…ُูˆุฑِ؛ ูุฅู†َّ ูƒู„َّ ุจุฏุนุฉ ุถู„ุงู„ุฉ)). ุฑูˆุงู‡ ุฃَุจُูˆ ุฏุงูˆุฏ ูˆุงู„ุชุฑู…ุฐูŠ، ูˆَู‚ุงู„َ: ((ุญุฏูŠุซ ุญุณู† ุตุญูŠุญ)). 


((ุงู„ู†َّูˆุงุฌุฐُ)) ุจุงู„ุฐุงู„ ุงู„ู…ุนุฌู…ุฉِ: ุงู„ุฃู†ูŠَุงุจُ، ูˆَู‚ِูŠู„َ: ุงู„ุฃุถْุฑุงุณُ.


Daga baban Najih Irbaadhi Bn Saariyata (R. A) yace : " Manzon Allah (S. A. W. W) yayi mana wa'azi, wa'azi mai ratsa zukata, zukata zuwa girgiza daga gare shi, idanuwa suka zubar da hawaye daga gare shi. Sai muka ce : " Yaa Ma'aikin Allah, kamar wa'azin bankwana?  To, kayi mana wasiyya.  Yace :


" INA YI MUKU WASIYYA DA TSORON ALLAH, DA JI DA KUMA BIYAYYA, KO DA AN SHUGABANTAR DA BAWA NE BAHABASHE A KANKU (ballantana kuma yaro).  DOMIN DUK WANDA YA RAYU (yayi nisan kwana) DAGA CIKINKU ZAIGA SASSABAWA MASU YAWA. (Idan hakan ta kasance) NA HORE KU DA BIN SUNNAHTA DA KUMA SUNNAR HALIFOFINA SHIRYAYYU MASU SHIRYARWA. KUYI RIQO DASU DA FIQOQINKU (with your canines). KUMA NA HANE KU DA FARARRUN AL'AMRA, DOMIN KOWACCE BID'AH 'BATA CE. "


Wannan ita ce wasiyyar Manzon Allah (S. A. W. W) wacce ya yiwa Sahabbansa  game da bin haqiqanin sunnarsa data Halifofinsa don sanin sassabawar da za a samu a cikinsu har zuwa kan na yanzu da muke raye .


Ba batu kan su waye wadannan Halifofi shiryayyu muke ba, shi yasa ba za muyi magana kansu ba. Amma dai sanin cewa ba guda hudun (4) nan ake magana ba shi yasa Umar Bn Khaddab yace LITTAFIN ALLAH KADAI MA YA ISHE SU BA SAI SUN BI SUNNAR ANNABI KO TA HALIFOFINSA BA. 


Da ace Umar ya san akwai shi cikin wadanda aka ce abi sunnarsu haqiqa da ba zai qyamaci  bin sunnah ba.


SHIN, HAR YANZU ANA KAN HAQIQANIN ABINDA ANNABI (S. A. W. W) YA BARI  ?


Kafin bada amsar wannan tambaya za muyi nazari muga shin, akwai wanda ya taba magana kan haka a baya ko kuma dai matsalar a wannan lokaci za a same ta? 


Anas Bn Malik na daya daga cikin Sahabban Annabi (S. A. W. W) wanda a duniyar Sunnah ake dogaro ko kafa hujja da labarin da ya bayar, duk da cewa ana samun qarya cikin zantukansa amma hakan ba zai zama dukkan zantukansa ne ke zama qarya ba, domin ana samun wadanda suka zo daidai da gaskiya. Ida gaskiya kuwa ko daga bakin shaidan (Satan) ta fito za a karbe ta, domin an gaskata maganarsa ranar AHZAB yayin da aka ganshi yana gudu har aka tambaye shi, sai yace lalle shi yaga abinda basu gani ba (Mala'iku). 


Imam Ahmad Bn Hambal ya kawo cikin Musnad nasa kamar haka :


11757- ุญَุฏَّุซَู†َุง ุฒِูŠَุงุฏُ ุจْู†ُ ุงู„ุฑَّุจِูŠุนِ ุฃَุจُูˆ ุฎِุฏَุงุดٍ ุงู„ْูŠُุญْู…َุฏِูŠُّ , ู‚َุงู„َ : ุณَู…ِุนْุชُ ุฃَุจَุง ุนِู…ْุฑَุงู†َ ุงู„ْุฌَูˆْู†ِูŠَّ ، ูŠَู‚ُูˆู„ُ : ุณَู…ِุนْุชُ ุฃَู†َุณَ ุจْู†َ ู…َุงู„ِูƒٍ ، ูŠَู‚ُูˆู„ُ : " ู…َุง ุฃَุนْุฑِูُ ุดَูŠْุฆًุง ุงู„ْูŠَูˆْู…َ ู…ِู…َّุง ูƒُู†َّุง ุนَู„َูŠْู‡ِ ุนَู„َู‰ ุนَู‡ْุฏِ ุฑَุณُูˆู„ِ ุงู„ู„َّู‡ِ ุตَู„َّู‰ ุงู„ู„َّู‡ُ ุนَู„َูŠْู‡ِ ูˆَุณَู„َّู…َ ، ู‚َุงู„َ : ู‚ُู„ْู†َุง ู„َู‡ُ : ูَุฃَูŠْู†َ ุงู„ุตَّู„َุงุฉُ ؟ ، ู‚َุงู„َ : ุฃَูˆَู„َู…ْ ุชَุตْู†َุนُูˆุง ูِูŠ ุงู„ุตَّู„َุงุฉِ ู…َุง ู‚َุฏْ ุนَู„ِู…ْุชُู…ْ ؟ " .


Ziyadu Bn Rebee'i Abu Khidaash Al-Yuhmadiyyi ya bamu labari yace : " Na ji Baban Imrana Al-Jauniyi yana cewa : " Na ji Anas Bn Malik yana cewa :


" BABU WANI ABU AYAU DANA SANI WANDA NASAN MUNA KANSA A ZAMANIN MANZON ALLAH (S. A. W. W). " Yace : " Sai muka ce masa, ina sallar ?" (Ma'ana kana nufi sallar da muke yi yanzu ba irin ta zamanin Annabi (S. A. W. W) bace)  ? (Anas)  Yace :


" YANZU KUNA AIKATA ABINDA KUKA SANI CIKIN SALLAH ?" (ma'ana abinda kuke yi yanzu cikin sallarku haka kuka santa zamanin Manzon Allah (S. A. W. W)  ?


  (MUSNAD AHMAD, HADISI MAI LAMBA 11757)


Idan muka kalli wannan magana ta Anas Bn Malik za muga abinda yake nunawa shine, duk wani abinda yasan ana yinsa zamanin Manzon Allah (S. A. W. W) an canza shi tun a lokacin Sahabbai, har ma sallah kanta kamar yadda ya tabbatar. 


TABBAS AN CANZA KOMAI 


Duk wani abu daka sani wanda Annabi (S. A. W. W) ya koyar yadda ake yinsa haqiqa an canza shi tun zamanin Sahabbai, kuma za mu bada misalai don kai ma kayi nazarin wannan babban lamari.


Cikin rubuce-rubucenmu na baya mun kawo misalai ne ta hanyar nassosi daga ayyukan manyan Sahabbai, amma yau misalai kawai za mu kawo ba tare da nassi ba.


(1)- RABON GADO  :-  Tun   daga wafatin Annabi (S. A. W. W) Abubakar ya saba ayar Al-Qur'ani wacce ta tabbatar da cewa 'ya'ya na gadon mahaifansu, kuma ya riqa shigar da wadanda basu da gado cikin magada. 


Umar ma yayi kaso mabambanta cikin mas'ala iri daya ba tare da samun wani bambanci cikin magadan ba, kuma akan wadannan hukuncin nasu aka tafi cikin rabon gado dake littafan Sunnah. 


(2)- AIKIN HAJJI :- Zamanin Annabi (S. A. W. W) yayi TAMATTU'I a aikin Hajjinsa, amma kuma zuwa lokacin shugabancin Usman Bn Affan sai ya hana. 


(3)- AZUMI :- 'Daukar azumi da shan ruwa dukka sunzo ne cikin Al-Qur'ani, kuma Annabi (S. A. W. W) ya koyar damu, sannan aka samu cikin Sahabbansa wadanda suka aikata kamar yadda ya koyar, amma daga baya sai aka canza daga yadda ya koyar, aka qirqiro hadisai aka zuba cikin littafan wadanda mafi yawan mutane suka koma kan wannan sabon canjin, ana shan ruwa kafin dare. 


Allah (T) na fada cikin Al-Qur'ani :


๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ


"...........ูˆَูƒُู„ُูˆุงْ ูˆَุงุดْุฑَุจُูˆุงْ ุญَุชَّู‰ ูŠَุชَุจَูŠَّู†َ ู„َูƒُู…ُ ุงู„ْุฎَูŠْุทُ ุงู„ุฃَุจْูŠَุถُ ู…ِู†َ ุงู„ْุฎَูŠْุทِ ุงู„ุฃَุณْูˆَุฏِ ู…ِู†َ ุงู„ْูَุฌْุฑِ ุซُู…َّ ุฃَุชِู…ُّูˆุงْ ุงู„ุตِّูŠَุงู…َ ุฅِู„َู‰ ุงู„َّู„ูŠْู„ِ............."


" ........... KUMA KUCI KU SHA HAR SAI HAR SAI FARIN ZARE YA BAYYANA GARE KU DAGA BAQIN ZARE, KUMA KU CIKA AZUMI ZUWA DARE..... "


     (BAQARA :187)


Ga misalin nan cikin Muwaddah Malik :


«641» ูˆَุญَุฏَّุซَู†ِูŠ ุนَู†ْ ู…َุงู„ِูƒٍ ุนَู†ِ ุงุจْู†ِ ุดِู‡َุงุจٍ ุนَู†ْ ุญُู…َูŠْุฏِ ุจْู†ِ ุนَุจْุฏِ ุงู„ุฑَّุญْู…َู†ِ ุฃَู†َّ ุนُู…َุฑَ ุจْู†َ ุงู„ْุฎَุทَّุงุจِ ูˆَุนُุซْู…َุงู†َ ุจْู†َ ุนَูَّุงู†َ ูƒَุงู†َุง ูŠُุตَู„ِّูŠَุงู†ِ ุงู„ْู…َุบْุฑِุจَ ุญِูŠู†َ ูŠَู†ْุธُุฑَุงู†ِ ุฅِู„َู‰ ุงู„ู„َّูŠْู„ِ ุงู„ุฃَุณْูˆَุฏِ ู‚َุจْู„َ ุฃَู†ْ ูŠُูْุทِุฑَุง ุซُู…َّ ูŠُูْุทِุฑَุงู†ِ ุจَุนْุฏَ ุงู„ุตَّู„ุงَุฉِ ูˆَุฐَู„ِูƒَ ูِูŠ ุฑَู…َุถَุงู†."


Abdul-Malik ya bani labari daga Malik daga Ibn Shihaab, daga Humaid Bn Abdurrahm cewa :


" LALLE UMAR BN KHADDAB DA USMAN BN AFFAN SUN KASANCE SUNA YIN SALLAR MAGRIB YAYIN DA SUKE SAURARON (zuwan) DUHUN DARE KAFIN SUYI BUDA -BAKI , SANNAN SUYI BUDA-BAKI BAYAN SALLAH, KUMA HAKAN A CIKIN RAMADANA (suke yi). "


(MUWADDAH MALIK, KITABUS-SIYAM) 


Yanzu kuma an cika duniya cewa kafin sallah ake shan ruwa, wai Annabi (S. A. W. W) ne ya fadi haka.


(4)- SALLAH :- Ita sallah kuma ita ce tafi muni wajen samun sassabawa, domin siffofin da ake yinta yanzu ba su da adadi. Misali :-


- Wasu sallama daya (1) suke yi. 


- Wasu biyu (2).


- Wasu su kama qirjinsu. 


- Wasu su sake hannayensu. 


- Wasu zaman hutu.


- Wasu sun dunqule hannaye yayin dagowa daga Sujadah. 


- Wasu su shimfida tafukansu.


- Wasu jiyarwa (ladanci). 


- Wasu babu jiyarwa.


                  D. S 


Idan ka tuntubi kowanne bangare sai yace maka wai haka Annabi (S.A. W. W) yake yi, kuma kowanne bangare na ganin shine ke bin haqiqanin sunnar Annabi (S. A. W. W) . Anya kuwa zai zama ya koyar damu abubuwan da zasu sanya mana sabani yadda kowa zai riqa gain dan'uwansa ba daidai yake yi ba  ?


Idan ka gamsu cewa an shiga rudani cikin ayyukan ibadu da hukunce-hukuncen, to, ta yaya za mu san haqiqanin sunnar tasa har ya zama mun dawo kanta don samun tsira gobe qiyama  ? Ko kuma dai haka za mu zauna alhali mun san an sami sabani daga koyarwar Manzon Allah (S. A. W. W) data Halifofinsa (A. S)  ?


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 


        (08137925034)


19th January, 2023/  27th Jimada-Sani, 1444.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post