HAR ANNABAWAN ALLAH SUNA NEMAN TAIMAKO A WAJEN WANIN ALLAH KUMA SUNE LIMAMAN TAUHIDI DA YAƘAR SHIRKA !!!

 1. Idan muka koma Alkur'ani cikin Surutun Namli aya ta 38-40 , za mu ga yadda Allah ya bada labarin Annabi Sulaimanu (a.s) Ya nemi taimakon mutanensa wajen zuwan masa da gadon mulkin Sarauniya Balƙisu kai tsaye , bai nemi taimakon Allah ba tare da shine limamin kaɗaita Allah na zamininsa , bayan Alhud-hud ya bashi labarinta da masaruatarta kai tsaye Annabi Sulaimanu (a.s) ya fuskanci mutanensa yana mai neman wanda yafi kowa saurin yanke zango domin yaje yazo masa da gadon Balƙisu , tun kafin tazo ita da jama'arta suna masu miƙa wuya , take wani Aljani yace  zai zo masa da gadon Mulkin kafin Annabi Sulaimanu ya tashi daga wurin zamansa , shi kuma Wazirinsa Asifu ɗan Barkhiya yace zai zo da gadon kafin Annabi Sulaimanu ya ƙifta idonsa.


قَالَ يَا أَيُّهَا الْمَلأ أَيُّكُمْ يَأْتِينِي بِعَرْشِهَا قَبْلَ أَنْ يَأْتُونِي مُسْلِمِينَ  قَالَ عِفْريتٌ مِنَ الْجِنِّ أَنَا آتِيكَ بِهِ قَبْلَ أَنْ تَقُومَ مِنْ مَقَامِكَ وَإِنِّي عَلَيْهِ لَقَوِيٌّ أَمِينٌ قَالَ الَّذِي عِنْدَهُ عِلْمٌ مِنَ الْكِتَابِ أَنَا آتِيكَ بِهِ قَبْلَ أَنْ يَرْتَدَّ إِلَيْكَ طَرْفُكَ فَلَمَّا رَآهُ مُسْتَقِرًّا عِنْدَهُ قَالَ هَذَا مِنْ فَضْلِ رَبِّي لِيَبْلُوَنِي أَأَشْكُرُ أَمْ أَكْفُرُ وَمَنْ شَكَرَ فَإِنَّمَا يَشْكُرُ لِنَفْسِهِ وَمَنْ كَفَرَ فَإِنَّ رَبِّي غَنِيٌّ كَرِيمٌ [سورة النمل:38-40].


A duk siyaƙin waɗannan Ayoyin bamu ji an ambaci sunan Allah ba kwata-kwata ballantana kuma a nemi taimakonsa wajen zuwa da gadon , kai tsaye Annabi Sulaimanu (a.s) ya nemi taimakon wanin Allah ne (Aljanu da Mutane ) , ban tunanin akwai wani Musulmi mai hankali da zai ce Annabi Sulaimanu bai san Allah ba ko yayi shirka da neman taimakon wanin Allah , bari ma abinda yayi shine ainihin Tauhidi don yasan abinda Asifu yayi bai yi shi ba sai da taimakon Allah da ikonsa , Asifu bai isa ya motsa ba da izinin Allah ba , tamkar mutum yaje wajen likita yayi masa magani yasan likitan nan bashi yake warkarwa ba Allah ne mai bayar da waraka a haƙika ba wani bawa ba , shi wanin Allah wasila ne kawai .


2. Haka nan a cikin sha'anin Annabi Isa ɗan Maryam (a.s) Allah ya bamu labari ; Yayin da Annabi Isa yaji kafirci daga garesu take sai yace waye zai taimakeni zuwa ga Allah ? Sai Hawariyyawa suka ce mune mataimaka Allah , munyi imani da Allah ka sheda lallai mu masu miƙawa wuya ne .


فَلَمَّا أَحَسَّ عِيسَىٰ مِنْهُمُ الْكُفْرَ قَالَ مَنْ أَنصَارِي إِلَى اللَّهِ ۖ قَالَ الْحَوَارِيُّونَ نَحْنُ أَنصَارُ اللَّهِ آمَنَّا بِاللَّهِ وَاشْهَدْ بِأَنَّا مُسْلِمُونَ  (آل عمران -52) .


Shima nan Annabi Isa (a.s) bai nemi iya taimakon Allah ba ya nemi taimakon wasu daga mutanensa ne , saboda ba kowanne neman yaimakon wanin Allah bane shirka ko kafirci , sai mutum yana ji cewa shi wannan da ya nemi taimako yana da cikakken cin gashin kansa a cikin taimakon da zai yi koma bayan na Allah shine ya zama shirka da kafirci , amma in ka nemi taimakon wanin Allah a matsayin tsani tare da ƙudirce mai taimako na haƙiƙa shine Allah wannan shine tsantsar imani , ta yanda za kaji kome yayi maka yayi maka bisa iko da mashi'ar Allah ba wai akan kansa ba .


3. A ƙissar Annabi Yusif (a.s) kuma Allah ya bamu labarin yanda Annabi Yusif ya bada rigarsa yace da ƴan uwansa in sunje su jefa rigar tasa a fuskar babansa zai dawo yana gani da idonsa tar, sannan su tattaro danginsu su zo masa dasu .


اذْهَبُوا بِقَمِيصِي هَٰذَا فَأَلْقُوهُ عَلَىٰ وَجْهِ أَبِي يَأْتِ بَصِيرًا وَأْتُونِي بِأَهْلِكُمْ أَجْمَعِينَ [ يوسف: 93] .


Shima nan bamu ji ance Annabi Yusif (a.s) ya ɗaga hannu yace ya Allah ka dawowa da babana ganinsa ba , kuma wannan abu da Annabi Yusif (a.s) ya umarce su suyi shine tsantsar Imani da Tauhidi .


Don haka neman taimako a wajen wanin Allah ko waye ba zai taɓa zama shirka da kafirci ba , har sai in mai neman taimakon ya ƙudirce mai taimakom a matsayin mai cikakken iko da mashi'a koma bayan Allah na Allah , duk mutum mai lafiyayyen hankali zai fahimci hakan Jawaki ne kawai basa fahimtar haka .


Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu 👏


✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey 


17 / Ramadan/1444H - 8/ 4 / 2023 Miladiyya.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post