LISSAFI MAI BAN TSORO GA RAYUWAR DAN ADAM !!!

 


A ɗauka za ka rayu shekara 100 cif a Duniya kan ka koma ga Allah Ta'ala , to bari muga shekaru 100 nan nawane shekarun da kayi rayuwa ta gaske a ciki .


Shekara nawa kayi kafin ka balaga Alƙalami ya hau kanka ?


Amsa : Shekara 15 , saura 85 .


To a cikin shekara 85 da suka rage ka lissafa da kanka :


1 . Shekara nawa kayi kana bacci a ɗauka kullum kana baccin awa 7 , sai ka lissafa bakwai sau 360 sannan kuma sau 85 sai ka kwashe adadin da ya baka a cikin shekara 85 nawa zai saura ?


2. Sai ka Lissafa adadin awannin da kake kwashewa a kullum kana sabgoginka na ƙashin kanka a rayuwa , daga nan ka lissafasu da adadin shekarun da suka rage cikin lissafin gaɓa ta daya (1) .


3. Sai kuma ka lissafa minti nawa kake kana cin Abinci a kullum a ɗauka awa daya da rabi kake yi , sai ka lissafata sau 360 sannan sau ta 85  tukunna ka kwashe Abinda ya rage cikin abinda yayi saura a gaɓa ta biyu (2) .


4. Ka lissafa shekara nawa kayi kana wasanni da shaholiyoyinka a cikin abinda ya rage a kashi na uku , sai ka kwashesu ka tsallaka gaba ta biyar a lissafin abinda ya rage .


5. Sai kazo ka lissafa kullum kana tafiyar da awa nawa wajen aikin alkhairi, Sallah , yin biyayya ga Allah da sauran aikin ɗa'a , sai kaga nawa ka samu , za kaga gabaƙi dayan shekarunta na haƙiƙa suna nan wanda kuma bai wuce ka ƙirgasu da yatsun hannunka ba .


To , yanzu ka rayu shekara 100 a Duniya amma kuma shekarunka na gaske a Duniya basu wuce ka ƙirga su da yatsun hannu ba kai kasan akwai ƙura , ballantana ma ba kowanne mutum bane zai yi shekara 100 a Duniya .


يَا أَيُّهَا الْإِنسَانُ إِنَّكَ كَادِحٌ إِلَىٰ رَبِّكَ كَدْحًا فَمُلَاقِيهِ


Na'am mutum mai wayo ko a cikin awa ɗaya rak zai iya yin aikin da zai zame masa alkhairi da albarka har ranar tashin Alƙiyama , Tom amma muna yin irin waɗannan ayyukan ko ba ruwanmu dasu , Allah mun tuba !


✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey 


Sha'aban/1444H - 6/3/2023 C.E.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post