NUSTEWAR KA'ABA A SHEKARA TA 1039H

  .A ranar 9 ga watan Sha’aban shekara ta 1039H ne aka yi Ambaliya a garin Makkatul Mukarramah, hakan ya kai ga nutsewar  dubban mutane kuma ruwan ya shafi katangar dakin Ka’aba har sai da ya ruguje gaba daya.


Bayan haka Babban Malamin nan Sayyid Zainul Abidin Al-Kashaniy Al-Hussainiy (ra) - Wanda ɗaya ne daga cikin daliban Mulla Muhammad Amin al-Istrabadi (Allah ya ƙara masa yarda) - ya tayar da harsashin ginin Ka'abar a lokacin yana rayuwa a kusa da dakin Ka'aba, shine daliln rubuta shahararren littafinsa mai suna mai suna :(مفرحة الأنام في تأسيس بيت الله الحرام) , wanda da kansa ya shiga aka sake jadadda ginin ɗakin Allah mai Alfarma.

Daga ƙarshe kuma ya yi Shahada a hannun Nasibawa (Makiya Ahlul Baiti) da suka yi masa kisan gilla a garin Makka .


✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey 


Sha'aban/1444H - 3/3/2023 C.E.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post