SHARUDAN DAKE INGANTA AZUMI KO BATA SHI ..!!



 HUKUNCE-HUKUNCEN AZUMI BISA KOYARWAR MUSLIMCI  !!!


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


SHARUDAN DAKE INGANTA AZUMI KO BATA SHI 


Bayan godiya ga Allah (T) daya nuna mana wannan wata na Ramadan mai alfarma muna fatan mu fara azumtarsa cikin lafiya mu qare shi cikin yardar Allah. 


Bayan wannan addu'ah za muyi wasu tsokaci ne game da hukunce-hukuncen azumi a muslimci da kuma kawo sharudan dake inganta shi. 


Da farko za mu fara da wannan aya dake cewa :


👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽


" أُحِلَّ لَكُمْ لَيْلَةَ الصِّيامِ الرَّفَثُ إِلى‏ نِسائِكُمْ هُنَّ لِباسٌ لَكُمْ وَ أَنْتُمْ لِباسٌ لَهُنَّ عَلِمَ اللَّهُ أَنَّكُمْ كُنْتُمْ تَخْتانُونَ أَنْفُسَكُمْ فَتابَ عَلَيْكُمْ وَ عَفا عَنْكُمْ فَالْآنَ بَاشِرُوهُنَّ وَ ابْتَغُوا ما كَتَبَ اللَّهُ لَكُمْ وَ كُلُوا وَ اشْرَبُوا حَتَّى يَتَبَيَّنَ لَكُمُ الْخَيْطُ الْأَبْيَضُ مِنَ الْخَيْطِ الْأَسْوَدِ مِنَ الْفَجْرِ ثُمَّ أَتِمُّوا الصِّيامَ إِلَى اللَّيْلِ وَ لا تُبَاشِرُوهُنَّ وَ أَنْتُمْ عاكِفُونَ فِي الْمَساجِدِ تِلْكَ حُدُودُ اللَّهِ فَلا تَقْرَبُوها كَذلِكَ يُبَيِّنُ اللَّهُ آياتِهِ لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمْ يَتَّقُونَ‏."


" AN HALATTA MUKU RUNGUMAR MATANKU A DARAREN RAMADANA, DOMIN SU SITIRA CE GARE KU, KU MA SITIRA CE GARE SU. ALLAH NA SANE DA CEWA KU KUN KASANCE KUNA HA'INTAR KANKU, TO, YA KARBI TUBANKU KUMA YA YAFE MUKU, YANZU KU RUNGUME SU (da nufin jima'i) KU NEMI ABINDA ALLAH YA RUBUTA MUKU. KUMA KU CI KU SHA HAR SAI FARIN ZARE YA BAYYANA GARE KU DAGA BAQIN ZARE NA DAGA ALFIJR, SA'AN NAN KU CIKA AZUMI ZUWA DARE. KUMA KADA KU RUNGUME SU ALHALI KUNA I'ITIKAFI CIKIN MASALLACI. WADANNAN SUNE DOKOKIN ALLAH KADA KU KUSANCE SU. KAMAR HAKA ALLAH KE BAYYANAR MUKU DA AYOYINSA GA MUTANE KO ZA SUYI TAQAWA. "


              ( البقرة: 187.)


Abinda ya faru shine akwai wadanda a farkon muslimci yayin da aka wajabta musu azumi kuma aka hana musu yin jima'i da matayensu yayin da suke azumi sai suka daukarwa kansu nisantar matansu gaba daya cikin watan azumi. Sai kuma aka samu daga cikinsu wadanda suke kusantar matan nasu bayan sun daukarwa kansu cewa ba za su kusance su ba. Shine Allah ke fada musu cewa ya halatta musu yin jima'i  da matayensu cikin dararen Ramadana, saboda haka su aikata ba tare da ha'intar kansu ba. 


Sannan kuma ya nuna musu cewa cikin daren nan ana iya cin abinci ba kamar yadda aka haramta musu da rana ba. Za suci su sha har sai alfijr na gaskiya ya bayyana gare su, daga nan sai su kame daga ci ko sha. 


Kalmar RAFASU na nufin jin jima'i ne, MUBASHARA kuma shine asalin runguma. Duk an haramta mana aikata su cikin yinin Ramadana. Duk wanda ya kasance su ya sabawa Allah. 



ABUBUWA BIYAR DAKE KARYA AZUMI 



الخصال ابْنُ الْوَلِيدِ عَنِ الصَّفَّارِ عَنِ الْبَرْقِيِّ عَنْ أَبِيهِ رَفَعَهُ إِلَى أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ: خَمْسَةُ أَشْيَاءَ تُفَطِّرُ الصَّائِمَ الْأَكْلُ وَ الشُّرْبُ وَ الْجِمَاعُ وَ الِارْتِمَاسُ فِي الْمَاءِ وَ الْكَذِبُ عَلَى اللَّهِ وَ عَلَى رَسُولِهِ وَ عَلَى الْأَئِمَّةِ ع‏."



Ya zo cikin Al-Kisaal na Ibn Waleed, daga Saffaari, daga Barqeeyi, daga babansa, ya daukaka (hadisin) zuwa ga Abu Abdullah (A. S) yace :


" ABUBUWA BIYAR SUNA KARYA AZUMI. 


- CI,


- SHA,


- JIMA'I, 


- NUTSEWA CIKIN RUWA,  DA 


- YIN QARYA GA ALLAH DA MANZONSA DA KUMA A'IMMA (A. S). "


الخصال ج 1 ص 137.


Sai dai kamar ci ko sha bisa mantawa ba sa karya azumi kamar yadda ya tabbata daga Manzon Allah (S. A. W. W). 


Ya zo cikin Ma'aanil-Akhbaar  na Quddanu kamar haka :



معاني الأخبار الْقَطَّانُ عَنِ ابْنِ زَكَرِيَّا عَنِ ابْنِ حَبِيبٍ عَنِ ابْنِ بُهْلُولٍ عَنْ أَبِي مُعَاوِيَةَ عَنْ سُلَيْمَانَ بْنِ مِهْرَانَ عَنْ عَبَايَةَ بْنِ رِبْعِيٍّ قَالَ: سَأَلْتُ ابْنَ عَبَّاسٍ عَنِ الصَّائِمِ يَجُوزُ لَهُ أَنْ يَحْتَجِمَ قَالَ نَعَمْ مَا لَمْ يَخْشَ ضَعْفاً عَلَى نَفْسِهِ قُلْتُ فَهَلْ تَنْقُضُ الْحِجَامَةُ صَوْمَهُ فَقَالَ لَا فَقُلْتُ فَمَا مَعْنَى قَوْلِ النَّبِيِّ ص حِينَ رَأَى مَنْ يَحْتَجِمُ فِي شَهْرِ رَمَضَانَ أَفْطَرَ الْحَاجِمُ وَ الْمَحْجُومُ فَقَالَ إِنَّمَا أَفْطَرَا لِأَنَّهُمَا تَسَابَّا وَ كَذَبَا فِي سَبِّهِمَا عَلَى نَبِيِّ اللَّهِ ص لَا لِلْحِجَامَةِ."


Daga Ibn Zakariyya, daga Ibn Habeeb, daga Ibn Buhluli, daga Abu Mu'awiyata, daga Sulaimana Bn Mihraaza, daga Abaayata Bn Rib'eyyu yace : Na tambayi Ibn Abbas (R. A)  game da mai azumi, ya inganta gare shi yayi Qaho ? Yace : 


" EH, MATUQAR BA YA JIN TSORON RAUNI (weak) AKAN KANSA. " Nace :


" To, shin Qaho zai iya warware masa azuminsa  ?" Yace :


" A'A ."


Nace : " To, menene ma'anar fadin Annabi Allah (S. A. W. W) yayin da yaga wanda ke yin Qaho cikin watan azumi cewa :


" AZUMIN MAI YIN QAHO DA WANDA AKA YAYI QAHON YA KARYE  ."


Sai (Ibn Abbas) yace :


" ABIN SANI (azumin nasu) YA KARYE NE SABODA SUNYI ZAGI KUMA SUN YI QARYA CIKIN ZAGIN NASU AKAN ANNABIN ALLAH (S. A. W. W), BA WAI DON  YIN QAHON BANE. "


معاني الأخبار: 165.


Abinda wannan hadisi ke karantar damu shine, yin Qaho cikin azumi ba ya karya azumi in har ba yin nasa ya cutar da shi bane. Amma in har yasan cewa zai iya cutuwa/galabaita sakamakon yin Qahon sai kuma yayi, to, azumin nasa ya karye. 



Riwayar da za mu kawo ta qarshe cikin wannan rubutu namu shine wacce tazo cikin Fiqhu na Ridha (A. S) kamar haka :



فقه الرضا عليه السلام‏ اجْتَنِبُوا شَمَّ الْمِسْكِ وَ الْكَافُورِ وَ الزَّعْفَرَانِ وَ لَا تُقَرَّبْ مِنَ الْأَنْفِ وَ اجْتَنِبِ الْمَسَّ وَ الْقُبْلَةَ وَ النَّظَرَ فَإِنَّهَا سَهْمٌ مِنْ سِهَامِ إِبْلِيسَ وَ احْذَرِ السِّوَاكَ الرَّطْبَ وَ إِدْخَالَ الْمَاءِ فِي فِيكَ لِلتَّلَذُّذِ فِي غَيْرِ وُضُوءٍ فَإِنْ دَخَلَ مِنْهُ شَيْ‏ءٌ فِي حَلْقِكَ فَقَدْ فَطَّرَكَ وَ عَلَيْكَ الْقَضَاءُ اجْتَنِبُوا الْغِيبَةَ غِيبَةَ الْمُؤْمِنِ وَ احْذَرِ النَّمِيمَةَ فَإِنَّهُمَا يُفَطِّرَانِ الصَّائِمَ وَ لَا غِيبَةَ لِلْفَاجِرِ وَ شَارِبِ الْخَمْرِ وَ اللَّاعِبِ بِالشِّطْرَنْجِ وَ الْقِمَارِ وَ لَا بَأْسَ لِلصَّائِمِ بِالْكُحْلِ وَ الْحِجَامَةِ وَ الدُّهْنِ وَ شَمِّ الرَّيْحَانِ خَلَا النَّرْجِسِ وَ اسْتِعْمَالِ الطِّيبِ مِنَ الْبَخُورِ وَ غَيْرِهِ مَا لَمْ يَصْعَدْ فِي أَنْفِهِ فَإِنَّهُ رُوِيَ أَنَّ الْبَخُورَ تُحْفَةُ الصَّائِمِ وَ لَا بَأْسَ لِلصَّائِمِ أَنْ يَتَذَوَّقَ الْقِدْرَ بِطَرَفِ لِسَانِهِ وَ يَزُقَّ الْفَرْخَ وَ يَمْضَغَ لِلطِّفْلِ الصَّغِيرِ فَإِذَا صُمْتَ فَعَلَيْكَ أَنْ تُظْهِرَ السَّكِينَةَ وَ الْوَقَارَ وَ لْيَصُمْ سَمْعُكَ وَ بَصَرُكَ عَمَّا لَا يَحِلُّ النَّظَرُ إِلَيْهِ وَ اجْتَنِبِ الْفُحْشَ مِنَ الْكَلَامِ وَ اتَّقِ فِي صَوْمِكَ خَمْسَةَ أَشْيَاءَ تُفَطِّرُكَ الْأَكْلَ وَ الشُّرْبَ وَ الْجِمَاعَ وَ الِارْتِمَاسَ فِي الْمَاءِ وَ الْكَذِبَ عَلَى اللَّهِ وَ عَلَى رَسُولِهِ وَ عَلَى الْأَئِمَّةِ ع وَ الخناء [الْخَنَا] مِنَ الْكَلَامِ وَ النَّظَرَ إِلَى مَا لَا يَجُوزُ وَ إِنْ نَسِيتَ فَأَكَلْتَ أَوْ شَرِبْتَ فَأَتِمَّ صَوْمَكَ وَ لَا قَضَاءَ عَلَيْكَ وَ لَا بَأْسَ أَنْ يَذُوقَ الطَّبَّاخُ الْمَرَقَةَ وَ هُوَ صَائِمٌ بِطَرَفِ لِسَانِهِ ."


Imam Ridha (A. S) na cewa :


" KA NISANCI SHAFA ALMISKI DA KAFUR DA ZA'AFARAN, KADA KA KUSANTAR DASU ZUWA GA HANCI. KUMA KA NISANCI SHAFA DA  SUMBA (kiss 😘 ) DA KUMA KALLO 😍, DOMIN SHI KIBIYA CE DAGA KIBIYOYIN SHAIDAN. 


KUMA KA TSORACI YIN ASHUWAKI DA 'DANYEN ABU, DA SHIGAR DA RUWA CIKIN BAKINKA DON KA JI DADI BA YAYIN ALWALA BA. DOMIN IDAN WANI ABU YA SHIGA CIKIN MAQOGORONKA HAQIQA AZUMINKA YA KARYE, KUMA AKWAI RAMAKO A KANKA. 


KA NISANCI YIN GIBA, GIBAR MUMINI, KUMA KA TSORACI ANNAMIMANCI, DOMIN SU (Giba da Annamimanci)  SUNA KARYA AZUMI. BABU GIBA GA FAJIRI DA MAI SHAN GIYA DA MAI WASA DA DARA DA CACA.


BABU LAIFI GA MAI AZUMI A SA KWALLI DA YIN QAHO DA SHAFA MAI DA KUMA SHAFA RAIHAAN, AMMA BANDA NARJISI (ban san ma'anar wannan kalma NARJISI da hausa ba). DA KUMA YIN WASA DA QURA DA WASUNSU BISA SON RAI MUTUQAR DAI BA ZA SU KAI GA HANCI BA, DOMIN AN RIWAITO CEWA ITA QURA  (mai kauri) TANA KARYA AZUMI (in an ganganta shigar da ita ta hanci ko baki ). 


KUMA BABU LAIFI GA MAI AZUMI YA 'DANDANA GISHIRI DA QARSHEN HARSHENSA 😜 YAJI YANAYIN 'DANDANON KUMA YA TOFAR. KUMA YA SAUQAQA (wannan dandanon) DOMIN QANANAN YARA .


IDAN KANA AZUMI, TO, YA KAMATA GARE KA LAZIMCI NUTSUWA DA TAKA-TSANTSAN, KUMA JINKA DA GANINKA SUYI AZUMI DAGA (gani ko jin) ABINDA BAI HALATTA GARE KA KALLE SHI BA .


KUMA KA NISANCI ALFASHA DAGA MAGANA, KUMA KA NISANCI ABUBUWA BIYAR DAGA AZUMINKA DOMIN ZA SU KARYA MAKA SHI :


CI, 


DA SHA, 


DA JIMA'I, 


DA NUTSEWA CIKIN RUWA,


DA KUMA YIN QARYA GA ALLAH DA MANZONSA DA KUMA A'IMMA (A. S). DA KUMA HA'INCI DAGA MAGANA, DA KALLO ZUWA GA ABINDA BAI INGANTA. 


IDAN KUMA KA MANTA HAR KACI KO KA SHA, SAI KA CIKA AZUMINKA, BABU RAMAKO A KANKA. KUMA BABU LAIFI (mutum) YA 'DANDANA DAFUWAR ROMO ALHALI KANA AZUMI (amma) DA  QARSHEN HARSHENSA. 



(1) علل الشرائع ج 2 ص 71.


(2) المحاسن ص 318.



YAA ALLAH KA BAMU IKON KIYAYE ABUBUWA DAKE KAIWA GA 'BATA AZUMI 


🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


           (08137925034)


22nd March, 2023/  30th Sha'aban, 1444.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post