Ɗaliban Makarantar Fudiyyah Nursery and Primary Saminaka sun shirya taron bikin Maulidin Sayyida Zahara tare da mijinta Imam Aliyu Dan Abu Dalib (As) !!!


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]  Ɗaliban Makarantar Fudiyyah Nursery and Primary Saminaka sun shirya taron bikin Maulidin Sayyida Zahara tare da mijinta Imam Aliyu Dan Abu Dalib (As) a haraban makarantar dake cikin garin Saminaka da yammacin yau Asabar 13 Rajab, 1444BH


Daliban makarantar sun gabatar da Kayatattun Shirye Shirye masu burgewa tare da nishadantarwa ton Taya Al'ummar musulmi murna da zagayowar ranakun haihuwar Imam Aliyu Dan Abu Dalib tare da matarsa Sayyida Fadima Az-Zahra (As)


Cikin abubuwan da Daliban makarantar suka gabatar sun hada da; welcoming songs address, Muhawara akan Ilimin Ya Mace, Muhimmancin neman Ilimi, Shirin Gidan TV akan Sayyida Fadima da Imam Ali bin Abu Dalib (As), Waken Yabo ga Malaman makarantar Fudiyyah da ita makarantar, Rawar Al'adun Gargajiya, Faretin Girmamwa, d's


Taron bikin Maulidin ya kayatar sosai ga mahalarta kowa sai ala Sam barka yake yi akan taron


Muna fatan Allah ya karama Malaman makarantar juriya da kokari wajen karantarwa, su kuma daliban makarantar Allah ya kara musu hazaka ya kuma basu ikon kiyaye abinda ake koyar dasu da kuma ikon aiki da shi Ilimin baki daya


Shaheed Nasir Abdulmalik

#MediaForumSaminaka

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post