Bakon Dakin Allah Haihuwar Imam Ali (A's) !!!

  



[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]

عَلِيّ بْن أَبِي طَالِب ; 


Imam Ali bn Abu Talib (AS) da ne ga baffan Manzon Allah (SAW) kana kuma mai kare shi wato Abu Talib da kuma Fatima bint Asad.


An haife shi ne a ranar Juma'a 13 ga watan Rajab shekara ta 30 bayan shekarar giwaye a dakin Ka'aba mai girma. Wanda Yazo Dai-dai Da Shekarata 600 Miladiyya. 


Shi dai Amirul Muminin (AS), kamar yadda dukkan bangarorin musulmi (Shi'a da Sunna) suka tabbatar, an haife shi ne a garin Makka a dakin Allah mai tsarki (wato dakin Ka'aba). Malumman Tarihi sun bayyana cewa, lokacin da mahaifiyarsa Fatima bint Asad ta fara jin alamun haihuwa nan take sai ta nufo dakin Allah mai tsarki. Ko da isowarta sai ta tsaya a jikin dakin tana mai addu'a ga Allah da kuma kaskastar da kai gare Shi don Ya saukaka mata wannan haihuwa ta ta, in da ta ke cewa:


"Ya Ubangiji na! Ni na kasance mai imani da kai da kuma dukkan litattafan da Ka saukar, da kuma dukkan Manzannin da Ka aiko, kuma na kasance mai gaskata maganarKa da kuma maganar kakana (Annabi) Ibrahim al-Khalil, wanda ya gina wannan daki na Ka. Ya Allah! Ina rokonKa don Annabawan Ka, Manzanni da kuma Mala'ikun Ka makusanta, da kuma don wannan jinjiri dake cikin cikina, da Ka saukaka min haihuwata"


Haka kuwa A kai a daidai lokacin ma tana cikin nitsuwa da kwanciyar hankali ne ba tare da wata damuwa ba ta Haifi Sayyidina Ali Ibn Abi Talib (AS)


Daga nan sai mahaifinsa Abu Talib ya gayyaci mutane don halartar walimar murnar wannan Kyauta da Allah Yayi masa da kuma dukkan halittun duniya.


Wannan haihuwa ta Imam Ali (AS) a dakin Allah al'amari ne da kusan dukkan malumman tarihi sun ruwaito shi da kuma tabbatar Dashi.


Abu Talib 


Abu talib jigo ne shi a cikin Kabilar Banu Hashim, Aihinin sunan Abu Talib shi ne Abdul Manaf, to amma an fi saninsa da wannan suna na Abu Talib hakan kuwa lakabi ne ake masa da babban dansa mai suna Talib. Shi dai Abu Talib baffa yake wa Manzon Allah (SAW) don shi dan'uwa ne shakiki wa Abdullahi baban Annabi (SAW). 


Kuma shi ne yaci gaba da kulawa da Annabi (SAW) har zuwa girmansa bayan rasuwar mahaifinsa Abdullahi da kuma kakansa Abdul Mutallib. Lalle tarihi ya tabbatar mana da irin tsananin kauna da soyayya da kuma kulawan da Abu Talib yake nuna wa Ma'aiki (SAW) sama da yadda yake nuna wa 'ya'yansa. Haka nan kuma bayan girmansa da kuma lokacin da aka aiko shi a matsayin Annabi, ya ci gaba da kare shi, har lokacin da Allah Ya karbi ransa, To saboda irin wannan kulawa nasa da kuma kariyar da yake bai wa Annabi (SAW) da kuma Musulunci ne ma yasa Manzon Allah (SAW) ya kira shekarar da ya rasu da suna "shekarar bakin ciki".


Fatima bint Asad 


Fatima bint Asad bn Hashim (RA) itace mahaifiyar Imam Ali (AS), kuma an ruwaito cewa ita ce Bahashimiya ta farko da ta auri wani Bahashime gaba da baya, kuma itace mahaifiyar sauran 'ya'yan Abu Talib, sannan kuma a hannunta ne Annabi (SAW) ya girma tana mai tsananin sonsa da kaunarsa kamar yadda mijinta yake masa. 


Don haka ne ma Annabi (SAW) yake ambatonta da cewa ita ce mahaifiyarsa. An ruwaito cewa tana daga cikin musulman farko, kana kuma wacce take da imani mai girman gaske, kana kuma ta yi hijira tare da shi zuwa Madina.


Sannan kuma an ruwaito cewa lokacin da ta rasu, Annabi (SAW) yayi mata likkafani da rigarsa, sannan kuma lokacin da aka zo tona kabarinta, shi da kansa ya tona ainihin ramin da za'a kwantar da ita a ciki, sannan kuma bayan ya gama ya kwanta a ciki yana cewa: "Ya Allah Ka gafarta wa mahaifiyata Fatima bint Asad kuma Ka fadada makomarta". 


An Ruwaito cewa, sahabbai (wasu sun ce Umar bn Khattab (RA) ne) sun tambayi Annabi (SAW) cewa me yasa ya aikata hakan don kuwa ba su ta ba ganin ya aikata hakan ga wani ba, sai yace musu; wannan mace ta kasance uwata ce bayan rasuwar ainihin mahaifiyata, kuna na rufe ta ne da riga ta, don ta kasance mata garkuwa ranar lahira, kana kuma na kwanta cikin kabarinta ne, don Allah Ya dada fadada mata shi da kuma hana kasa matse ta, don kuwa ta kasance mafi kyautata min cikin bayin Allah bayan Abu Talib".

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post