-->
Barka Da Zuwa Shafin Ma'asumah Nigerian News Update
5 Ga February; Shakaru  5 Dai-dai da Shahadar  Shaikh Qashin Umar .

5 Ga February; Shakaru 5 Dai-dai da Shahadar Shaikh Qashin Umar .

 


A rana mai kamar yau, 5 ga watan February 2018 ne Shaikh Qaseem Umar ya riski Shahada, bayan ya shafe kusan wata guda yana jinyar raunin harbin da Jami'an tsaron Nijeriya sukai masa.


Jami'an 'Yan sanda sun harbi Shaikh Qaseem tare da wasu yan uwa a yayin da suke gabatar da Muzaharar kira a saki Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky, a ranar Talata, 9/1/2018 a garin Abuja.


Tsawon kwanaki kimanin 26 Shaikh Qaseem na fama da jinyar harbin da aka masa da harsashi mai guba, inda a ranar Litinin 5/2/2018 Allah Ya karbi rayuwarsa.


A ranar Laraba 7/2/2018 ne dubun-dubatar al'ummar Musulmi suka hadu a birnin Shehu, Sokoto, inda suka shaidi janazar Shahid Qasim, wanda aka bizne shi a gidansa da ke garin Sokoto din.


Shahid Qaseem ya kasance daga mabiya Jagora, Shaikh Zakzaky da gaskiya, ma'abocin sallamawa da ba da gudummawa ga Harkar Musulunci ta kowane janibi, ya samu shaida daga dukkan yan uwa akan cewa shi tsayayye ne a kan duk al'amari ko kokarin da zai yi sanadin kubutar Jagora daga ko ina hakan ya zo.


Bayan shahadarsa, tare da cewa dukkan yan uwa da ma al'ummar Musulmi sun koka, amma sauran bangarorin Harkar Musulunci, musamman bangaren masu tsarawa da gudanar da Muzaharar Abuja (Abuja Struggle), da mawallafan ayyukan Jagora, wanda aka fi sani da Cibiyar Wallafa da yada ayyukan Shaikh Zakzaky, suna kukan musamman kan rashinsa a duk sadda suka gaza riskar irin gudummawar da yake badawa ta janibinsu.


Bawan Allah da ya samu kyakkyawar shaida daga mahaifiyarsa, yan uwansa da al'umma daban-daban, musamman makwafta, Jagora (H) ga matukar kaduwa tare da damuwa da rashinsa, inda ya yabe shi da tsayuwa da sallamawa.


Allah Ya girmama matsayinsa. Ya tsinewa makasansu albarka. Ya tabbatar da mu a tafarkin da suka tafi suka bar mu.


— Saifullahi M. Kabir

5/2/2020.


Maimaici daga shekarar 2020

0 Response to "5 Ga February; Shakaru 5 Dai-dai da Shahadar Shaikh Qashin Umar ."

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa