Emefiele ya kai kansa gaban majalisar wakilan Najeriya !!!

 
[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


Gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele ya bayyana a gaban majalisar wakilan kasar wadda ta dade tana nemansa kan rudanin da sauyin tsofaffin takardun naira da sababbinsu ya haifar.


Emefiele ya bayyana ne a gaban kwamitin bincike na wucin gadi da majalisar ta kafa, wanda shugaban masu rinjaye na majalisar Ado Alhassan Doguwa ke jagoranta.


A makonnin baya, kakakin maalisar Femi Gbajabiamila, ya aika wa Emefiele da wani sammaci, kuma ya bukaci jami'an 'yan sanda su kamo shi bayan da yayi biris da gayyatar da majalisar ta dade tana mika masa kan batun.


Majalisar ta jinkirta tafiya hutu domin zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisa, wanda ta so tafiya tun ranar Alhamis.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post