Bankuna Za Su Ci Gaba Da Karɓar Tsaffin Takardun Kuɗi Bayan Wa’adin Kwanaki !!!

 


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


Gwamnan babban bankin Najeriya ya bayyana wa majalisar Tarayya cewa bankunan kasuwanci na kasa za su ci gaba da karbar tsoffin kudi bayan wa’adin da bankin ya saka na 10 ga Faburairu.


Gwamna Emefiele ya kara da cewa, daga yanzu zuwa 10 ga wata da shine ranar karshe da za rika amsar kudi don cinikayya na na daram sai dai kuma maida tsoffin kudin zai ci gaba har bayan wannan lokaci.


Majalisar Tarayya ta gayyaci Emefile ya bayyana a gabanta domin yayi mata bayani kan canjin takardun kudi da kuma wa’adin ranar da za dakatar da amfani da su.


Yadda kwamitin majalisar Tarayya ta ki amincewa da wa’adin kwanaki 10


Kwamitin Majalisar Tarayya ya ce kwanaki goman da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ya ƙara kan ci gaba da canjin kuɗi, sun yi kaɗan, kuma rainin wayau ne.


Shugaban kwamiti Honorabul Ado Doguwa ya ce talas Emefiele ya dokar Najeriya, ko kuma su sa a kama shi.


Ya ce tilas Emefiele ya bi Sashe na 20 na Dokar CBN, ko kuma ya fuskanci fushin majalisa.


A ranar Lahadi ce Emefiele ya yi sanarwar ƙarin wa’adin kwanaki 10, bayan ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari a Daura.


Yanzu a cewar sa, za a daina karɓar tsoffin kuɗaɗe a ranar 10 Ga Fabrairu.


PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda wani lauya ya maka CBN kotu, ya na neman a tsawaita lokacin daina karɓar tsoffin kuɗaɗe.


Wani lauya mai suna Joshua Alobo, ya maka Babban Bankin Najeriya (CBN) kotu, inda ya nemi kotu ta soke wa’adin ranar 31 Ga Janairu da CBN ya bayar, a matsayin ranar daina amfani da tsoffin nairori.


Alobo, wanda farfesa ne a fannin lauya da shari’a, ya nemi Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke ranar da CBN ta bayar, wato 31 Ga Janairu a matsayin ranar daina karɓar tsoffin kuɗaɗe.


Kuɗaɗen da CBN ya sauya wa launi dai sun haɗa da takardun naira 1,000, takardun naira 500 da takardun naira 200.


Hususan dai shi mai ƙara ya roƙi kotu ta umarci CBN ya ƙara wa’adin daina amfani da tsoffin kuɗaɗen da aka sauya wa launi zuwa ƙarin makonni uku yadda sabbin takardun nairori.”


Waɗanda lauyan ya maka kotu sun haɗa da CBN, Gwamnan CBN Godwin Emefiele da kuma Antoni Janar na Tarayya, wanda shi ne Ministan Harkokin Shari’a.


Alobo ya aika da kwafen bayanan sa ta hannun lauya Musa Damudi, mai ɗauke da bayanin cewa an ƙaddamar da amfani da sabbin N1,000, N200 da N500 a ranar 26 Oktoba, 2022.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post