WAJIBI NE SANIN HADAFIN HARKA ISLAMIYYAH




Inji Shaikh Ibraheem Zakzaky (H):


"To shi kenan dai, abin da muke cewa yanzu shi ne, mishkilar da muke fuskanta shi ne, akwai wani ana tafiya da shi a Harka din, amma shi bai  san ta inda aka dauko ba, bai san inda aka je ba. Saboda haka shi ya zo da wata fahimta tasa ta daban, to mai irin wannan fahimtar sai ya zauna, tun da abin da ya wuce, shi bai sani ba, da wuyar gaske da ya zama ya cafa ya yi kyakkyawar fahimta ga abun, sai ya tafi a haka nan.


"Alal misali, akwai wata da aka tambaye ta, me ya sa take Harka? Sai ta ce (saboda) Son Ahlul Baiti! ‘Good enough’, amma ban tsammanin ta fahimci abun sosai ba. Don haka yake da kyau irin wadannan Mu’utamarori, manufar Mu’utamarorin shi ne, a samu a kwakkwafa fikira, don ita fikira tana cigaba. Bari in muku misali da batun canzawa din nan, menene canzawa?Canzawa shi ne kana abu ka fasa, ka yi wani abu daban. Alal misali da yanzu za a ce, sai mu ce yanzu dai gwagwarmayar nan dai ta ishe mu, kocikin wadannan Pipopi za mu shiga daya, ko kuma za mu kafa ta mu (jam’iyyar). Ko mu shiga APC ko mu kafa MBC, sai a ce, ah me za ku yi? sai mu ce za mu tsayar da dan takara ne, yanzu sunan mu ‘yan MBC.  Shi kenan sai a ce MBC, sai a ce yeeeeeh! A tsayar da dan takara kawai a yi ta ihu.


"To wannan in dan Kwamashiyal ya ga dama, sai ya ce ahaf, sun canza, sun koma suna Siyasa. To ka ga sosai canji ne wannan, tun da yake da can ga abin da ake yi, yanzu kuma an koma an ce za a tsaya takara ne.


"Ko kuma mu ce gaskiyar al’amari shi ne, yanzu mun ga wannan al’amari da dan wahala, yanzu a shiga a gyara. Tun da akwai batun ‘yan a shiga a gyara, don akwai masu wannan ra’ayin,  ba mu san ina ‘yan a shiga a gyara suka shiga ba, ko sun gyaggyaru ne ba mu sani ba. Shi ma sai a ce ai a baya ga ra’ayin su, amma yanzu kuma sun daina, sun daina sam-sam, sun koma sun ce da su za a dama abin da ake damawa. ‘Yan Siyasa suna da wannan, har ma suna da wani slogan, ‘If you cannot defeat them, join them’, wato wa

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post