Cutar Dundumi Ko Ganin Hazo-Hazo A Idanu...!!!


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


Cutar dundumi ɗaya ce daga cikin larurorin dakan shafi idanu. Wannan larura ce ta dakushewar kaifi/ƙarfin gani, yanda mutum shi akaran kansa ke tabbatarwa da kansa yana da larurar domin baya bukatar zuwa wajen likita yin gwaji kafin ganota. 


Masu wannan larurar galibi in sun zo wajen likita sukan ce likita gani na baida kyau, idona ina jin kamar an zubamin mai acikin sa, dususu nake ganin abubuwa ba irin tar-tar ba kamar da. Bawai duhu mutum yake gani ba.... a'ah yana ganin komi fes saide ba tar ba, abubuwa musamman manya kamar Motoci, gini, ko wani symbol duk yana ganinsu normal, amma kuma bai iya ganin rubutun jikin symbol ɗin fes-fes musamman in ƙanana ne bazasu karantu da kyau ba, zai iya ganin sun harhaɗe musamman in kwai yar tazara. 


Wani lokacin sukan gani da kyau idan rana ta take, toh amma in yamma tayi musamman gefin magriba duhun nan nasa ganin nasu yai dususu sosai har sai daren ya taho anyi sallar magariba sai kyawun ganin nasu ya qaru. Wanda ke da wannan larurar nasan zaifi fahimtar me nake bayani da kyau.


______________________________________


Jiya nasa wasu hotuna inda nake tambayar tsakanin "A" da "B" wanne yafi fita fes? Inda dukkan masu gaskiya batare da son raurawar zuciya ba suka tabbar da hoton "A" yafi "B" fita, wanda tabbas hakan ne, ai baka bukatar ma yin wani tunani abu ne a fili, kai da gani kasani. 


Don haka wanda suka zaɓi "B" bamu san meke damun idonsu ba, ƙila ko don ni nace "B" shiyasa suka zaɓi su bar gaskiya su ma su rufta rami 😊


Nayi wannan tambayar ajiya ne kafin kawo wannan karatun don kowa ya fahimta. Sashin 'A' ɗin shine yadda mutane masu "Normal vision" wato kaifin gani ke kallon abubuwa, yayin da shi kuma "B" ɗin tamkar hakane masu larurar dundumi ko gani hazo-hazo (blurry vision) ke ganin abubuwa, wato ga abin a haskake saide ba fes ba kamar de hotunan jiya da kuma na qasa jikin hoton ƙasan post dinnan.


______________________________________


Ita wannan larura ta rarrabu zuwa muhimman gidaje guda biyu; 


1- Mai ganin hazo-hazo, dundumi-dundumi ko garara-garara daga nesa, wato "Short ko Near sighted" a turance, ko ince MAYOFIYA a yaren likitanci (mayopia). da kuma


2. Mai ganin hazo-hazo, dundumi-dundumi ko garara-garara daga kusa, wato "Long ko Far sighted" a turance, ko ace HAIFAMETIROFIYA a yaren likitanci (Hypermetropia).


Dukkan biyu dinnan abu iri guda idanunsu ke nuna musu. saide


_____________________________________


MAYOFIYA: Masu wannan su suna iya ganin duk abinda yake kusa dasu fes wanda nisan sa dashi bai wuce taku goma ba "10feet", yana iya karatu da rubutu normal. Inda matsalarsu take kurum in suka kallo abinda ke nesa sai suga baya fita sosai, ko fuskar mutum ce basa iya ganinsa fes sai ya matso kusa, haka ko TV suke kallo saide su zauna agaba kamar de yadda hotunan nan suka nuna. Yayin da shi kuma me


HAIFAMETROFIYA: suna iya ganin duk abinda ke nesa fes-fes kamar wata daren 14, amma kuma in abun kusa kusa dasu yake dab' basa iya gani da kyau. Wato a me wannan matsalar shi abinda ke nesa kurum yake iya gani da kyau. Wadannan sunfi shan wuya wajen karatu a littafi ko sarrafa wayoyin hannu domin Baƙaƙen har haɗe musu suke, kaga mutum nata takure ido, har idanu suke zafi.


Shiyasa galibi za kuga malamai da medicated glass, ko manyan yan boko har ariqa farar paper ta cinye musu ido, ba'a gani sai ansa glass. 


Wasu zasu iya ma komi batare da glass ba toh amma zarar sun dau littafi to sai sun nemosa sun saka, shiyasa wasu sai zasui karatu suke sakawa.


______________________________________


MEKE HADDASA MATSALAR


1. Wannan matsala takan bi cikin family wato ya zamto gado ce akai daga iyaye da kakanni, shiyasa sau tari koda a finafinan turawa zaku ke ganin yara ƙanana sanye da tubaran ƙara ƙarfin gani wato medicated glass, haka muma anan bazaku rasa ganin yara masu sanya glass ba kullum, Cikin manya kuwa wannan kusan kowa ya gani, kwai yan Mata da Maza yan kwalisa ma kuwa amma duk suna sanya glass ko yaushe saboda ganin su, prescription glasses ne ballantana iyayen mu dattawa ko manyan malamai.


2. Canzawar girman ƙwayar ido wato eye ball, ta yadda tai girma ta kuma tsuke takai ga ko ido ya kallo abu wannan abin bai tsirgawa har cikin retina saide ya yanke dab da tsayin da ya saba tunda kwayar idon ce ta matsa baya, shi kuma karfin yadda ido ya dauko abin bazai iya qetare yadda ya saba ya isa can ba. Shine abin ke yankewa kaga dususu.


3. Kwai yawan zama cikin daki musamman inda duhu kwana da kwanaki babu fita aga rana saide kallon screen ko yaushe, wannan ma na taɓa ido. Shyasa galibi a wanda suka je prison ake cewa ansasu a ɗakin duhu zaku ga wasu in sun fito suna samun matsala da ganin su.


4. Shekaru, Eh mana daga sanda aka ba 40yrs baya karfin gani galibi kan canza, saide wani canjin yafi bayyana sosai bayan an cimma 50yrs.



Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post