JERIN GWANON AMFANIN ZUMA*** Zuma na Daya Daga Cikin Kwari Masu amfani da yawa a rayuwar Dan Adam, inda amfanin ta ya fara tun daga kan ruwan ta, wato kashin zuman, da ita kanta zumarGa kadan daga cikin muhumman amfanin zuma ga lafiyar dan Adam :-

1. Zuma na kare mutane daga kamuwa da cutar siga wato Diabetes da turanci sannan kuma yana hana tashin cutar wa mutanen da ke fama da shi.
2. Zuma na maganin mura, kawar da matsalolin da ke kama ido kamar jan ido, kaikayin ido,kumburin ido da sauransu.
3. Zuma na kuma warkar da rauni ko kuma kuna a jikin mutum.
4. Zuma na rage yawn mantuwa musamman matan da suka daina haihuwa.
5. Yana kuma maganin cutar Ulcer.
6. Zuma na warkar da cutar dake kama hakarkari wato Pneumonia da turanci.
7. Zuma na taimaka wa mutanen(maza ko mata) dake fama da matsalar rashin haihuwa.
8. Zuma na kuma maganin ciwon ciki.
9. Zuma na gyara fatar mutum.
10. Zuma na warkar da tari.

Zuma Zumunci
Haka nan yana daga cikin sirrin zuma ana shan zuma a hadata da citta koda yaushe domin

  • Maganin Sanyi
  • gyaran murya
  • maganin Athsam
  • Maganin Tari
  • maganin majinar kirji
  • Maganin Ciwon Ciki

Sai dai wadannan suna da kyau kasha da Ruwan Zafi domin Samun cikakken Amfani.

Cututtukan Zuciya
Haka nan yana daya daga sirrin da zuma take tattare dashi don magance cutukan zuciya. Za'a samu lafiyayyen nono a hada da zuma da ma'u kal fari a hadasu asha cokali biyu safe da yamma Inshaallahu

Domin maganin Basir
A samu zuma kamar Robar yaghort, A hada da Garin Hulba babban Cokali 2 na cin Abinci, sai kwaba so da ruwa dan kadan karamin ludde na roba. Sai a sha bayan an chakuda Cokali 2 Sau ukku Ayini Sannan Sai ayi masti da Jubda Kamar Sau 2 Ayini.


Maganin Ulcer
A kwaba zuma da hulba da Habbatus saudah a yinka sha babban Cokali 2 Sau ukku ayini kafin aci abinci na kowana lokaci.

Bissalam Allah Sa Mudace Ameen !


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post