Alhamdulillah A Yau Laraba 25 ga Jimadal Thani Allah Ya Azurta Wasu daga cikin Almajiran Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da suke Karatu a Karbala Al-Muqaddasa a

 


Makarantar  Ma'ahad Warisul Anbiyya ,  samun Sanya Rawani a hannun Shugaban Haramin Imamu Hussain Wakilin Marji’iya Sheikh Abdul Mahdi Al-Karbala’i An Sanya Rawanin Ne Karkashin Jagorancin Shugaban Makarantar Sheikh Ahmad Amily.


Cikin Farin ciki aka gabatar da sanya musu  Rawanin tare da tayasu murna da Kuma Musu Nasiha akan Wajiban da suka hau kansu bisa wannan Nauyi daya hau kansu.


Sudai Wadannan Yan uwan Mutun 12  dukkanin su Almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky (H) ne.


Sannan Akwai Wasu Daliban da suke karatu Anan Yan Ghana Suma duk Sun samu Sanya Rawanin .


Muna alfahari da ku. Allah Ya yawaita mana ire-irenku cikin almajiran Sayyid Zakzaky (H).

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post