Amfanin Hasken Rana Ga Lafiyar Ƙashi Da Gaɓoɓi...!


 

@MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE. 


- By Dr Nazir Muhammad Umar... ✍️ 

Fatar jikin mutum na amfani da hasken rana domin samar da sinadarin bitamin D wanda muhimmin sinadari ne wajen gina lafiyayyen ƙashi da gaɓoɓi. 

Lokacin sanyi ko hunturu hasken rana zuwa ga muhalli yana raguwa. Saboda haka, akwai barazanar fuskantar ƙarancin bitamin D lokacin sanyi.

Shan hasken rana musamman lokacin sanyi na taimakawa kauce wa barazanar ƙarancin sinadarin bitamin D lokacin sanyi. Saboda haka, shan hasken rana na taimakawa gina lafiyayyen ƙashi da gaɓoɓi.

Bugu da ƙari, shan hasken rana na taimakawa kiyaye tashi ko ta'azzarar ciwon gaɓoɓi lokacin sanyi.

Anfi samun wannan sinadarin Vit D din dasafe 9amto 11am. Allah Yasa Mudace. 🙏

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARAN MU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

Shiga Group din mu na Telegram Anan

👉 @MA'ASUMAH TV TELEGRAM

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/maasumahNews/

DOMIN BA DA SHAWARA KO AIKO DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post