Jami'in Tsaron Falasdinu Ya Yi Shahada A Nablus Da Ke Gabar Yammacin Kogin Jordan.
-Bin Muhammad

2023-01-18 H.TV


An yi arangama tsakanin sojojin gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila da Falasdinawa a birnin Nablus da ke gabar yammacin Kogin Jordan.


Rahotonni sun bayyana cewa: Sojojin gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai farmaki kan yankin da ke gabashin birnin Nablus a shiyar arewa maso yamma da gabar yammacin kogin Jordan, inda suka fuskanci mayar da martani daga Falasdinawa, don haka suka bude wutar bindiga tare da harba iskar gas mai guba kan al’ummar yankin.


Kamar yadda ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta ce: Sojojin mamayar gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila sun harbe wani jami'in tsaron Hukumar cin kwarya-kwaryar gashin kan Falasdinawa a yankin arewacin garin Khalil lamarin da ya sanya yawan Falasdinawan da suka yi shahada suka haura zuwa 15 tun daga farkon wannan sabuwar shekara ta 2023.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post