GANGAMI DOMIN TUNAWA DA KISAN KIYASHIN ZARIA A GARIN DAURA

 


Ranar Assabar 8 ga watan Disambar shekarar 2022, Ƴan-uwa almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky (H) a garin Daura, sun gudanar da Gangami domin tunawa da Kisan kiyashin da sojojin Najeriya suka yi a Zaria a shekar 2015, wanda a ƙalla aka rasa rayuka aƙalla sama da dubu (1000+).A shekarar dubu biyu da goma sha biyar (2015), Gwamnatin Buhari ta aiwatar da mummunan ta'addanci akan ƴan-uwa almajiran Malam Zakzaky (H). An yi kisan kiyashin da ba a taɓa ganin irinsa ba a tarihin duniya, domin an kashe yara, tsofaffi, har da jarirai ba bisa wani haƙƙi ba, bisa tsabar tsagwaron tantagaryar Zalunci.


An fara wannan mummunar aika-aika ne tun 12 ga watan 12 na shekarar 2015 har izuwa 14 ga wata, wato dai tsawon kwana biyu ana aikata ta'addanci a kan mutanen da ba su ji ba su gani ba. An harbi wasu da dama daga cikin almajiran Malam (H) harbi na rashin imani, an ƙone wasu da rai, an kuma kama wasu an kullesu saboda zalunci.#kisankiyashinzaria 

#ZariaMassacre 


A A Wisdom Daura 

09/12/2022.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post