RAN MUTUM DAYA YAFI KA'ABA, GARA A RUSHE KA'ABA DA A KASHE RAN MUTUM DAYA ! _Shaikh Ibraheem Zakzaky (h)

 



—Sheikh Ibraheem El-Zakzaky (H) 2009

Malam ya karanto wani hadisul kudusi cewa
Yazo A Hadisul Kudusi Allah (T) yace: " da za'a tambayeni : ace da za'a kashe ran mutum daya 1  mutum kuma yace, baice muminiba, da akashe mutum daya da a rubde (Rushe) saman bakwai zuwa kasa ba mutum, Allah (T) yace da za'a tambayeni wannene zan yarda ?!, da sai ince gara a rushe sama da kasa har saman bakwai 7 da akashe man Ran mutum daya 1, domin mutum nayishi nakuma zartar da cewa in an kasheshi , bazan dawo dashiba sai tashin kiyama, ita kau wannan duniyar da kunfa yakun tariga, in an rusa zan iya maida'ita "

sheikh bai tsaya nan ba saida yasake karanto man Hadisin manzon Allah (s.a.w.w) cewa : manzo (s.a.w.w)  ya dubi ka'aba yace  data:  "ما اعظمك" wato  "ya girmanki yake wannan ka'aba" Allah ya girmamaki amma ran mumini daya 1 ya fiki .

shekin malamin yace : yanzun da za'ah tambayeka, da akashe Ran mumini guda daya 1 da a rubde (Rushe) ka'aba wanne yafi sauki ? sai kace gara a Rubde ka'aba  domin rushe ka'aba za'ah iya maidawa

malam ya sake kafa hujja da ayar Allah yace: Allah ya cewa :
" وَمَنْ يَقْتُلْ مُؤْمِنًا مُتَعَمِّدًا فَجَزَاؤُهُ جَهَنَّمُ خَالِدًا فِيهَا وَغَضِبَ اللَّهُ عَلَيْهِ وَلَعَنَهُ وَأَعَدَّ لَهُ عَذَابًا عَظِيمًا"

wanda duk ya kashe mumini da gangan saka makosa jahannama zai dawwama a ciki kuma Allah yayi fushi dashi, yayi mashi tanadin babbar azaba abinda muka fahimta babbar azaba din nan hattama bayan jahannma dinnan akwai wani kari, ehmana! فَجَزَاؤُهُ جَهَنَّمُ  sai yace وَأَعَدَّ لَهُ عَذَابًا عَظِيمًا ai kaga shima birbishin jahannama din ne

sayyid yacigaba da cewa: kashe mutum ba karamin al'amari bane, ko bisa al'ada mutanenmu suna da wani abu wannan kamar sannen abu ne, cewa: duk wanda yayi kisan kai baya gamawa lapia.

wani dan tambihi da ni mai rubutu zanyi akai shine, kui dubo izuwa ga Azzalumai masu sawa a kashe mutane  ya karshen su yake ? karshensu bai yin kyau, misali sani Abacha ya karshensa ya kasance ? ,

DAGA:- Ibraheem S.F. Yankara

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post