MENE NE MAFITAR MUSULMIN NIGERIA A WANNAN HALIN DA MUKE CIKI? _Shaikh Ibraheem Zakzaky (h)

 


— Shaikh Ibraheem Zakzaky yace:

"Bani bukatar na dauki lokaci ina mana bayanin yadda wannan kasa (Nijeriya) ta kasance. Kowa ya sani. Ko sai na ce muku ga halin da take ciki?

Sai na ce muku ba amana? Ba aminci a kan hanyoyi, bashi a gidaje bashi a sararin samaniya? Sai na fada muku cewa ba ruwan famfo, ba man fetur, ba wutar lantarki? Ko sai na fada muku akwai ramuka a kan hanya? Ko sai na ce muku ana fama da rashin aikin yi? Ko sai na ce muku dabi'u sun lalace? Duk kun san wannan. Kowa yana ji jika!

Ko sai na fada muku cewa makarantu ba komai, sun zama gidajen kadangaru? Ko sai na fada muku cewa asibitocin Kasar nan sun zama makasa, gidajen kisa, a kai ka a karisa ka!?... In ana maganan matsalolin kasar nan kowa ya sani, kuma kowa yana ji a jika. Amma yanzu mene ne mafita?

Kwanan nan za a yi wani shiririta, wai zabe. Na san wadannan tsinannun, wadannan 'yan iska din! Ba wani zaben da za su yi. Wannan' ya'yan iskan, club din ya'yan banza, tsinannu, Allah Ya kara tsine musu. Mu kam wallahi bamu yafewa masu rike da al'amarin kasar nan ba! Bamu yafe musu ba. Allah (T) Ya sa su yi mummunan karshe a duniya. Allah Ya dauwamar da ya'yan banza a wuta. Hakkinmu kuma Allah Ya fitar mana. Bamu yafe ba Wallahi. Musibar da kuma muke zaune a ciki Allah Ya isa! Kuma muna rokon Allah (T) Ya gaggauta kawo mummunan karshen wadanda suke mulkin kasar nan.

Nigeria ce kawai kasar da tsinannu suke mulki, sai fitaccen fasiki, dan iska ake ba mukami a kasar nan. Wanda basu san kowa da komai ba sai kawukansu kawai. Ba wanda za ka duba a cikinsu ka ga al'umma ta dame shi, su kansu kawai suka sani, yaci ya sha yai facaka, ya kwashe arziki ya kai kasar waje. Wai za su yi zabe.

Yanzu abin takaici sai Kaga mutane ana kada su duu kamar shanu, wai za a yi zabe, ba wani zaben da za su yi. In ma zabe ne da wannan bakin da wancan bakin wane bakin kake so? Ka duba ka ga wannan baki ka kalli wancan ma baki. Ka dawo ka duba ko wannan baki-baki ne, ka ganshi bakin kirin, ka duba wancan ka ganshi kirin kin-kin, ka rasa na dauka a ciki. Dukkansu bakake masu bakar aniya da muguwar zuciya. Wai an baka zabi ka dauki daya daga cikinsu.

To, mu sani cewa mafitarmu sam bashi a katin kuri'a, duk wani da kaji yana fada maka (mafitarka na katin kuri'arka) ko Malam ne, to bai san inda duniya ta saka ma gaba ba. Mafitarmu bata a katin kuri'a. Katin kuri'a ba zai baka dama ba illa ka zabi wannan fasikin ko wancan fasikin. Wannan macucin ko wancan macucin. Amma maceci ba zabensa za a yi ba, da karfin tsiya za a dankara shi!

Abin da ke gabanmu shine bore na bamu yarda ba! Ni ban san har wani lokaci za a kai ba, komai akai ma mutane su yi shiru, an dauke wuta ana fama da zafi, suce Kaga tsinannun na basu kawo wuta ba ko? Shikenan. Kaga shegun nan basu kawo ruwa ba, tsinannu. Zuwa can in an kawo mutane suce Kaga ma tabo suka turo mana. Shikenan ya zauna shiru. Ana nan rashin lafiya ya same shi ya je asibiti ya wuni ba a duba shi ba, ko an zurma masa allura ciwo ya karu, ashe magani ya kare. Sai dai ace Kaga wadannan dai yadda suka kashe wane, Allah dai ya isa. Shikenan.

Anya haka za a cigaba? Su wadannan azzaluman an fada muku haka ya dame su ne? In dai za ku zauna ku yi shiru, to kuwa za a cigaba. Abin da ke gabanmu bore ne na bamu yarda ba! Har sai sun ga uwar bari! Ba kuma wai su gyaru ne ba, a'a har kowane tsinanne ya san mafitarsa, ya haura katanga! In tsinanne ya ji an kewaye gidansa ya ce akwai hanyar fita? Aka ce ai ba kofa ta baya, sai ya haura katanga. Shine kawai. Kuma ko an ki ko an so, abin da zai fitar da mu kenan. Ba wata hanya!

Shi ya fitar da al'ummun da kuka ga sun samu sauyi, musulmi suke ko ba musulmi ba. Wadanda suka samu sauyi daga danniyar azzaluman da suke mulkin Kasarsu, ba sun zauna ne ba, ba kuma sun ka da kuri'a ne ba. Yaushe azzalumin da ke shugabantar kasa zai ce yanzu shi ke da akwatun zabe, shi ke da katin zabe, yace ka zo ka zaba ka fitar da shi? Ai ba zai yiwu ba. Kai zabe ka fidda shi? Ba zai yiwu ba. Ko ka kada kuri'a sai dai in Damina ne ka sha dukkan ruwa, in irin yanzu ne ka sha rana ka kada, a karanta abin da aka ga dama.

Ko ba komai ma tun farko an baka zabi tsakanin wane ne? Su suka zaba maka duk wadanda za ka zaba din. Kai naka ka kada ne, wannan kake so ko wancan. Ka duba ka gansu duk cikansu macuta. To wanne kake so ya cuce ka? Sai kace to, da wancan ya cuce ni gara dan gidanmu? Yanzu abin da mutane suke cewa kenan, kullum waye nasu? Waye dan gidansu ko dan kabilansu, ko dan garinsu? Zancen banza! Don Allah da macijin gidanku ya sareka ka mutu, da macijin waje ya sareka ka mutu ina bambamci? Wannan kafiso ya sare ka cikin macijan nan biyu? Akwai bambanci? Da kumurcin gidanku da kumurcin gidan wani duk kumurtai ne!

Amma an dauke hankalin mutane da waye dan garinsu? Waye dan gidansu. Waye dan bangarensu? Waye dan jiharsu? Da shine kawai ake jan su. Shikenan sai ka ji suna mu dai muna goyon bayan wane. In kace wannan ba alkairi bane. Suce kai dai kawai kama hassada ne, mu dai Allah ya ba dan gidanmu ko ma samu muma. Ka ji suna cewa da dan gidan wani gara dan gidanku. Wannan ko Jahiliyyar Larabawa da suke dore a kan wasu abubuwa na Aklaq basu yi lalacewar haka ba. Su suna duba wane ne mutumin kirki. Na'am suna da zafin Kabilanci, amma ba su kan yarda mai mummunan dabi'a ya shige gabansu a wurare da dama ba. Amma nan waye nasu kawai.

To wannan baganniya na zabe don mu sani, ba inda zai kai mu. Abin da ya kamata al'ummar Musulmi su sani shine dama can su jam'iyya ce. Basu bukatar Pi-Po-Pin nan! Basu bukatar PPP ko PA-PA-PA Ko Wasu jam'iyyu. Jam'iyyarmu dama akwai ta. Meye sunan jam'iyyarmu? Musulunci. Wannan jam'iyya kuwa ba wanda ya kai ta yawa. Meye Akidar wannan jam'iyya? Musulunci.

Yanzu kuna tsammanin al'ummar Musulmi da za su dake kyam suce basu yadda wani abu ya yi iko da mu ba in banda addininmu. Akwai wani wanda ya isa ya dora musu wani abu ba Musulunci ba? 

Amma yanzu baganniyar da al'ummar nan ta shiga kenan, cewa gashi yau shekara da shekaru da barin wannan Manzo (S) duniya, amma ga yan al'ummarsa ana ta kada su kamar shanu. Sun kasa gane cewa addininsu za su dauka su rike kam. Manzon Allah (S) za su dauka a matsayin abin koyi su yi koyi da shi, shine mafita a gare su."

— Shaikh Ibraheem Zakzaky a jawabin rufe Muzaharar Mauludin Annabi (S) ranar 17 ga Rabi'ul Auwal 1428 (2007).
-Cibiyar Wallafa.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post