FIR'AUNA RAMZI NE, BA JIKI BA

 



Shamsudeen Hassan

Fir'auna ya zama Fir'auna da Taimakon Mutanenshi. Su suka bashi Aron Tunaninsu, sai ya zamo shi ke musu Tunani, su kuma su aikata. Haka ta faru ne Saboda sun kasa sabunta Tunani, sun Damfarewa Hanyar Iyaye da Kakanni Idon Rufe. Sai ya zamo Kwakwalwa bata ja, batada Nauyi.

Allah yace: فاستخف قومه فأطاعوه

Wato basu masa biyayya ba, sai bayan da ya rena Hankalinsu, ya rena musu wayo, sannan ya dinga Kadasu kamar Shanu.

To yadda Fir'auna ya rena Hankalin Mutanenshi haka 'Yan Siyasar Kasar Hausa suka rena Hankalin Mutanensu. Haka Malaman Kasar Hausa suka Rena Hankalin Mabiyansu.

Sai suka zamo Fir'aunoni, suna juya Akalar Tunanin Mutanensu kamar Rakuma. Su ke masu tsari, su ke Qullawa,  su ke Walwalewa.

Sun kai Hankalin Hausawa Injury, Sun bawa Tunaninsu Hutu, sun Dakushe musu Kwakwalwa,  sun kashe masu Zuciya...
Su ko basu da aiki sai biyayyah kamar Dabbobi,  koma fiye.

Ga Zukata amma basu iya Tunani da su, Ga Idanu amma basu iya gani dasu,  ga kunnuwa amma basu iya ji dasu.

Shi yasa duk wani Maceci sunansa Macuci a wajensu, saboda a haka Fir'unonisu za su nuna masu shi. Su kuma basu iya gane cewa ba haka bane, saboda babu Tunani, ba Hankali,  ba La'akari,  ba Tadabburi.
إن هم إلا كالأنعام بل هم أضل...

Duk Al-ummarda bata iya yima kanta Tunanin Makoma, to ka yanke kauna daga Dagawarta zuwa kololuwar Saqafa da Hadara da Madaniyyah.

Ka yanke Kauna daga fitarsu cikin Ququmin Bauta, da Mamayar Magauta, koda ko ance su 'Yantattune. 'Yancin nasu baya wuce saman Takarda.


https://t.me/Drshamsudden

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post