AMAKON DA YA GABATA AKA GUDANAR DA MUZAHARAR MAULUDI MANZON RAHMA (S) A GARIN KUDAN @_Ma'asumah Nigeria News update

 


“ Yan 'uwa Musulmi almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky ( H ) dake garin kudan suka gudanar da Bikin mauludin Manzo Allah ( S ); dubban mutane masoya Manzon Allah daga garuwa irin su Kaduna, Zaria, Soba, Samurun Zaria, kagara Jahar Katsina, Rogo, da magari, makarfi, Hunkuyi,  Dabai, Danja. Suka halarci taron Bikin tunawa da ranar Manzon Rahama ( S )..

Bayan sauke muzaharar Maulud, 'yan fodiyya sun gudanar da faretin girmamawa ga Manzon Allah, haka zalika kuma Jawabin rufe muzaharar Wanda wakilin 'yan uwa nagarin Kudan. Malam Junaidu Muhammad Sani Kudan ya gudanar Jawabin akan Manzo Allah ( S ) wanda ya yi sa a taƙaice inda ya ce jawabin Maulud sai zuwa anjima wanda Shaikh Yaqoub zai ga batar.

 Jawabin Maulud daga babban baƙo: Shaikh Yaqoub Yahya Katsina.

Shehin malamin ya fara da cewa Manzon Allah Yazo Ne Domin Ya Shiryatar Da Al'umma Ne, Ta Yadda Zai Zama Addinin Musulunci Shike Saman (Iko) Addinin Yahudu Da Nasara.

Ya ƙara da cewa: Officially Yanzu Gwamnatin Ƙasar Saudiyya Ta Tabbatar Da Mauludin a Cikin Jerin Bukukuwan Da Za a Riƙa Gabatarwa Duk Shekara.

Bayan kammala raba kyaututtuka na wasan ƙwallon ƙafa wanda Shaikh Abdulhamid Bello Zaria ya fara ga Batarwa da matakin farko. Na raba kyaututtuka tare da karama wasu daga ciki. 

“ Shaikh Yaqoub Yahya: shi ne ya raba kyautar ba da kofin ƙwallon ƙafa wadda aka saka gasa na Halƙoƙin dake Da'irar Kudan, Shehin malamin ya ba da kyauta ta farko ga waɗanda suka zo na farko Halƙal Imam Aliyu Zainul-Abideen, ne suka zo na ɗaya wanda Shaikh Yaqoub. Ya raba kyautar ga zakarun wasa.

   GANAWA DA YAN UWA 

Ganawar Shaikh Ya'aqoub Yahya Katsina Da Yan Uwa na Da'irar Kudan.

Da safiyar yau Alhamis 17/11/2022, Shaikh Ya'aqoub Yahya Katsina ya gana da yan uwa almajiran Shaikh Zakzaky(H) na Da'irar Kudan. Ganawar data kebanta da yan uwa (Khasatan) na Da'irar, wacce ta hada yan uwa maza da mata a cikin Husainiyyah Kudan.

A cikin ganawar, Malam ya karfafi yan uwa dangane da Harkar Ilimi, inda a cikin jawabin nasa yake cewa; "Yanzu al'umma gaba daya mune fatanta, yanzu al'amarin yana ta kara fadi, sabida haka ya kamata ya kasance muna da Malamai sosai wadandu zasu rike bangarori wajan shiryar da al'umma. Kada ya kasance malamanmu na baya dai har yanzu sune malaman. Lallai mu baiwa wannan fannin muhimmanci domin dama da wannan din ne (ilimi) harkar ta doru a kai.

Sannan ya karfafi yan uwa akan abinda ya shafi tattalin  arziki, inda yake cewa, Ya kamata ace muna da wasu hanyoyi na musamman da muke samun mashigar kuɗi, kada ya zamana cewa mun dogara ne da hanya kwara ta Infaki. Har ya bada misalin cewa da ace Da'ira zata samar da wani tsari kamar Noman rani ko kiwon Kaji da ko wani abu dai makamancin haka, da an samu cigaba sosai da rage bukata daga yan uwa na Imfaki wajan gudanar da wasu abubuwan. 

Da yake nasiha ga yan uwa kuma, ya nasihanci yan uwa dangane da soyayyar juna, da aiki domin Allah. Yace "Mu daina kallon yan uwa, kowa ya kalli kansa, mu daina kallon cewa wane yana da matsala, kai dai ka dubi kanka. Harkar nan bata bata da wani matsala, mu na cikin Harkar ne muke da matsala, domin tun daga farkor harka har zuwa yanzu babu abinda ya canja na daga Hadafi ko Fikhira. Tun daga Sallalolin Nafila, azumin Litini da Alhamis, Zikiri da Salatin Annabi, Sanya Hijabi, babu abinda ya canja. Alhalin duk wadannan sune asasin abubuwan da harka ta doru a kai Alkur'ani da Sunnar Annabi."

Daga karshe, Malam Ya yi addu'ar tabbatuwa a wannan Harka wacce Malam Zakzaky ke yiwa jagoranci har zuwa shahadarmu.

Ƙarshen rahoton ke nan daga.

Abbakar Ibraheem Kudan

Faruq Sani Kudan

Ma'asumah Nigeria News update

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post