Wacece ta Dace na Aura

Bismillahir-rahmanir-rahiim..✍️ 

 Babban burin kowane Namiji shine,samun Mace ta gari. A kullum tsakanin Mata da Maza addu'ar su da ta masoyansu in ana batun abokin zama to babban fatan shi ne samun abokin zama nagari. Amma da dama masu neman wannan abokin zaman na kwarai basu damu da su zama nagarin ba.

 To abin daurin kai shine,Ta yaya za a samu wannan hadin na iyalai masu daraja in har halayensu bai zo daya ba? A rayuwar aure kowa da irin hakki da Kason nauyin da yake dauka,namiji kan zama ginshiki mai tsawatarwa da shiryarwa da sa ido da sauran nauye-nauye narayuwar iyalinsa,Inda mace kuma ke kula da gida ta kula da Mijin,ta gyara,ta inganta alakarsa da iyaye Yan'uwansa,In an samu zuriya ta kula da ingancin walwalarsu da tarbiyyarsu. Hatta mu'amalar mijin ta kasuwa ko office da nutsuwarta ya ke samun nasara.To in kuwa haka ne,To waya fi dacewa da ya zamo nagari da farko? Ko wane dan Adam yana da burin ya zabi mace ta gari koda kuwa shi ba namiji na gari bane Domin kowa ya yarda cewa mace ta gari alheri ce ga mijinta. Kamar yadda yazo,a hadisin Manzon Allah(S) Cewa; Duniya gidan jin dadice, amma mafi alkhairin abin jin dadin duniya itace mace ta gari. _Manzon Allah(S) Yace; "Ana auren mace dan abubuwa guda 4,sune,KYAU,DUKIYA,NASABA,ADDINI.Sai yace; Amma ina kwadaitar muku da ku auri me ADDINI. To Amma sai yazamana wasu daga cikin Mazajenmu na yanzu,sun fiye maida hankulansu wajen zabar Mace mai,DUKIYA,NASABA,da kuma KYAU.Sun bar me ADDININ,Wanda Manzon Allah(S) Ya kwadaitar gare su,dasu auresu. Sai dai kuma abinda basu ganeba shine,Matuqar ka auri Mace,dan👇 

= DUKIYARTA. To bai zama lallai kaci moriyarta da ranta ba,bare bayan ranta,dan ba ko wane me kudi ne ke taimakon Sirikinsa ya masa hanyar arziki ba,Kuma ma da za kayi hakuri arzikinka na bibiye dakai kamar yanda ajalinka ke bibiyarka.Lokaci kawai yake jira. Sannan koda ka Zai zama kai da gidanka,amma tafika iko da gadara da gidan,har ma yazama kamar itace mijin kaine matar,gadararta ka aureta ne dan dukiyarta. Dan'uwa,ina so kasani cewa,ita dukiya zata iya qarewa ta barka.= MACE MAI NASABA Babban burinka ka auri mace me Nasaba,Ace wance ''Yar wane,jikar wane,kai shine burinka da jin dadinka,ita kuma tana ganin cewa'masu sha'awar Aurenta 'Yan neman suna ne da son Alfarma.Sai kayi abinda kake so Aganinka zata zame maka Garkuwa. To bari kaji, Iyakaci kaci albarkacinta Alokacinda take da rai ne kadai,kuma Ita dai 'Yar dangi har gara Mata masu Dukiya da ita,damin maiyiwuwa a cikinsu asamu wanda zasu bar SADAKA. Sannan itama za'a iya wayan gari yazama bata da kowa nata,dik sun mace,Allah ya rufa asiri.

= MACE KYAKYKYAWA Da yawan maza sun fi son Mace fara kyakkyawa,To ga shi dai maza sunfi Sha'awarta,Amma sam-sam babu wani abin Amfana'atare da'ita.Watakila ace ta haifi 'ya'ya Kyawawa,gashi tahaifo su dakyau kuma babu tarbiyya,sun zama fitina ga Al'umma,to yanzu ina riba anan ? Har gara 'Yar dangi da ita,dan qila ita riba ce,baza a samu daga wajentaba,amma ita Naqsuce za'asamu atare da ita,Domin zama da ita Fitina ne da kuma damuwa,idan har bata da tarbiyyah. Ina so musani cewa; Shi kyau yana iya gushewa ta hanyoyi da yawa,yana iya yiwuwa tsautsayi ya iya fadawa kan wannan kyakkyawan fiskar da surar ta ta,har yazama kyan nata ya baci. Sannan akwai tsufa,akwai mutuwa,domin idan ta rasu,duk farin fatarta,da tsawon gashinta da hancinta da kuma surarta,haka za'a binne ta da kayanta,tunda dai baza a ciri kyan nata amanna maka shi agoshinka ko'Yayanka da sunan gado ba.

 = MACE MAI ADDINI. Ita ce wacce Manzon Allah(S) Ya kwadaitar da'asameta Amatsayin matar aure. Domin ta tattara abubuwa dayawa;ILIMI,WAYEWA,HANKALI,NUTSUWA, Da sauransu. Amma'annan kuma ana Amfana da ita ko da ta rasa wadancan ababe,(KYAU,DUKIYA,NASABA), Sai tafi soyuwa Awurin Allah,tafi soyuwa awurin halittunsa na sama da kasa. "Shi dai Allah Ba ya duba zuwa ga halittarku yana duba ne zuwa ga zukatanku" inji Manzon Allah(S). Su kuwa bayin Allah sun fi son zama da son jin motsin wanda suke karuwa dashi.Ilimin da ta bayar ba ya taba lalacewa,dan idan ta koyawa ma wani,shima zai koya ma wani,To da haka za'aita tafiya,Munga kenan ko anan ma ta bada gudumawarta ga Al'umma ba ga 'Ya 'yanka kadaiba. Ya kai dan'uwa me daraja,kasani hakkine akanka kanemar wa 'Ya'yanka Uwa ta gari,babu wacce tafi cancanta da hakan illah mace ta gari,Mai Addini. Insha Allah,Anan zamu dakata. Allah Yasa mudace. 

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com



Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post