Hukumci daga ayoyin Alqur'ani kan jifan Mazinaci ...Fita ta Ɗaya (1)


 

Da farko inaso mai karatu yagane yadda Allah yayi bayanin hukuncin wanda yayi zina, mai aurene ko mara aure duk hukuncinsu daya acikin Alqurani Suratun Nur. Kafin yafara maganar hukuncin sai da Allah yace :


سُورَةٌ أَنْزَلْنَاهَا وَفَرَضْنَاهَا وَأَنْزَلْنَا فِيهَا آيَاتٍ بَيِّنَاتٍ لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ


“Wannan surar mun saukar da ita kuma mun farlanta (aiki da ita), sannan mun saukar da ayoyi bayyanannu acikinta don ku fadaka ” ((Nur : 1))


ABIN DUBA : Allah acikin wannan surar tun farko sai da yayi bayanin cewa zai saukar da surar da wajibine ayi amfani da ita kuma yace ayoyin cikinta bayyanannu ne don so ake kowa yayi aiki da ita don yafadaka. Kuma surar an saukar da itane bayan anyiwa Nana Aisha (ra) sharrin cewa tayi zina, kaga macece mai aure sai Allah tun kafin ya kubutar da ita daga sharrin da akayimata sai yafara bada hukuncin wanda akace yayi zina mai aurene ko mara aure, sai yake cewa :


الزَّانِيَةُ وَالزَّانِي فَاجْلِدُوا كُلَّ وَاحِدٍ مِنْهُمَا مِائَةَ جَلْدَةٍ وَلَا تَأْخُذْكُمْ بِهِمَا رَأْفَةٌ فِي دِينِ اللَّهِ إِنْ كُنْتُمْ تُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ وَلْيَشْهَدْ عَذَابَهُمَا طَائِفَةٌ مِنَ الْمُؤْمِنِين


“Mai zina mace da mai zina namiji kuyiwa dukansu bulala dari, kuma kada kuji tausayinsu akan bin (hukuncin) Allah indai kunyi imani da Allah da ranar lahira, kuma jamaar muminai su halarci azabar da zaayimusu ” ((Nur: 2))


Acikin wannan ayar Allah yayi bayanin duk hukuncin mazinata kiri kiri kuma bazaka taba samun wata ayar acikin Qurani data saba da wannan ba. Sai dai ace wai akwai ayar rajamu da aka shafe karatunta amma hukuncinta yananan!


Sheikh Ahmad bn Siddiq Algumariy (rh) acikin littafinsa ” Budlani Nuskhit tilawa” yana cewa : “babu hikima akan cewa anshafe aya yayinda zaace hukuncinta kuma yananan, sannan kuma ace ayar da aka shafe din wai tananan”. Sannan abin mamakin shine shifa hadisin da ake kafa hujja dashi wajen jifan mazinata bai kai haddin tawaturi ba. Suko ayoyin Alqurani gaba dayansu mutawaturaine, to bansan ta ina zaace hadisin da baikai tawaturi ba har zai shafe ayoyi!


Abinda mutane basu saniba shine, hukuncin rajamu yasamo asaline daga yahudawan da suka shiga musulinci suka sako hukuncin aciki. Domin idan kaduba Bible zakaga hukuncin acikin “old testament”! To da sukaga ba yadda zasuyi su canja Alqurani sai sukaga bara suce anshafe ayar kuma wai da hadisi!


Dama Allah yabamu labari acikin Qurani inda yake cewa Manzon Allah (saw) zai kai kara gunsa kan Alummarsa da suka watsar da hukunce hukuncen Alqurani suka tsaya kewaye kewaye. Kuma wannan matsalar ta shafi yan Ahlussunnah da kuma Yan Shia akan hukuncin rajamu, inbanda wanda Allah yakare daga “mufakkirai” na musulinci da “muhaqqiqai”.


Akwai bayanai dayawa da zanyi akan wannan hukuncin na #rajamu da batancinsa a musulinci wanda zai warware shubuhohin aikatashi da kuma rushe hadisan da sukazo dashi insha Allah, ku biyoni anan gaba.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post