@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
HADDIN KISA NA ZUWA NE QARSHEN KOWANNE HADDI
Hukunci ba ya yiwuwa sai da ilimi, kuma zartar dashi ba bisa ilima ba kan zama zalunci ga wanda aka yiwa da kuma wanda ya zartar.
Idan aka sami mutum ya aikata laifuffuka mabambanta wadanda suka cancanci haddi, to, akan fara ne daga qarami zuwa kana babba.
Ga yadda ake yin haddi ga wanda aka same shi da laifuffuka uku na shan Giya da sata da kuma zina.
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
1- ب، قرب الإسناد عَنْ عَلِيٍّ عَنْ أَخِيهِ ع قَالَ: سَأَلْتُهُ عَنْ رَجُلٍ أُخِذَ وَ عَلَيْهِ ثَلَاثَةُ حُدُودٍ الْخَمْرُ وَ الزِّنَا وَ السَّرِقَةُ بِأَيِّهَا يُبْدَأُ مِنَ الْحُدُودِ قَالَ بِحَدِّ الْخَمْرِ ثُمَّ السَّرِقَةِ ثُمَّ الزِّنَا[1].
Daga Aliyu, daga dan'uwansa (A. S) yace, anyi tambaya kan mutumin da aka same shi da haddodi uku;
Giya,
Zina, da kuma
Sata .
Da wanne za a fara cikin haddodin? Yace,
" DA HADDIN GIYA, SANNAN SATA, SANNAN ZINA ."
(1) نوادر الراونديّ ص 33 و ما بين العلامتين ساقط من الأصل.
(2) قرب الإسناد ص 112 ط حجر
NAZARI
Idan muka kalli wadannan laifuffuka guda uku za muga cewa, an fara ne da hukuncin mai shan giya domin haddin da ya hau kansa shine bulala.
Hukuncin sata kuwa shine yanke hannu gwargwadon yadda shari'a ta bayyanar.
Ita kuwa zina haddin kisa ne ga wanda ya kasance muhsini ko muhsina.
Saboda haka idan an fara da kisa an zalunce shi.
.
و في دعائم الإسلام ج 2 ص 464، عن عليّ عليه السلام أن رجلا رفع إليه قد أصاب حدا و وجب عليه القتل فأقام عليه الحدّ فقتله قال أبو جعفر عليه السلام: و كذلك لو اجتمعت عليه حدود كثيرة فيها القتل لكان يبدأ بالحدود التي دون القتل، ثمّ يقتل.
Cikin wannan littafi mai suna na sama kuwa, daga Imam Aliyu (A. S) cewa wani mutum ya zo gare shi da laifin da haddinsa shine kisa, sai Imam (A. S) ya zartar masa da hukuncin kisa.
Abu Ja'afar (A. S) yace,
" TO, KAMAR HAKANE , DA ACE HADDODI ZA SU HADU A KANSA WANDA CIKINSU AKWAI KISA, TO, ZA A FARA NE DA HADDIN DA BAI KAI (girman) KISA BA, SANNAN KISA ."
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
24th December, 2020/ 10th Jimada-Ulah, 1442.