Shugaban Qasa Muhammadu Buhari Ya Cika Shaikaru Saba'in da Takwas (78) Marasa Albarka.



Tsawon shaikaru 78 da shugaban ya kwashe yana rayuwa a duniya bai tsinanawa kansa komi na Alkhairih ba, balle kuma ya tsinanawa al'umma da har zasuyi alfahari dashi. Tarihi ya tabbatar da irin mummunan halayyar sa tun farkon rayuwarsa, ta yadda har zuwa yanzu hakan yake babu abinda ya rage na cuta da zalumci, illa ma kari da yayi akan hakan.


A iyaka sanin da duniya tayiwa Buhari lallai babu wani abin fada na kwarai da za'a fada a kansa, domin tun daga kasancewarsa shugaban kasa a karo na farko babu abinda al'umma ke fade a kansa illa Alla-wadai da suke tofawa a mulkinsa, sakamakon irin ci baya daya jawo wa kasa da al'ummar kasa.


Haka ma dai abin yaci gaba da guduna har zuwa wannan lokaci da al'umma musamman matasa sukayi zaton cewa kamar shine mafita a garesu, amma sai dai kuma kash ! abinda su zata ba shine ya biyo baya ba. Domin kuwa babu wanda baisan irin mummunan halin da buhari ya jefa wannan kasa da al'ummar ta ba.


Baya ga mummunan ta'addanci da shugaban ya aukar ga shugaban yan Shi'a (Sayyeed Zakzaky h.) da al'amajiransa a zaria ashaikarar 2015. Kimanin fiye da shaikaru biyar da suka wuce, karkashin jagorancin Tukur Yusuf Burutai da yaransa (sojojin najeriya). Wanda hakan ya jawo wa wannan kasa bakin jini da Alla-wadai daga dukkan sassa na duniya.


Har ila yau wannan kasa da al'ummar ta basu fita daga tarkon Buhari na kangin talauci daya sanya su ba. Yanzu a wannan kasa Najeriya taulauci, raunana harkar ilimi, raunana harkar lafiya, raunana harkar abinci, yawaitar ta'addanci, kashe-kashe, garkuwa da mutane, gurbatar tarbiyya, duk wadannan sun zamo ruwan dare a cikin al'ummar najeriya. 


Buhari ya janyo wa wannan kasa ci baya da nakasu da aibu, ta yadda kullum daraja da farin jininsa raguwa take ga al'ummar kasa. Ta yaya wanda yayi wadannan ayyuka masu muni ya cancanci ya zamo shugaban al'umma ? Tabbas Buhari bai shuka komi a rayuwarsa ba tun daga yarintarsa har zuwa tsufarsa. Kuma da sannu zai girbi abinda ya shuka nan kusa bada jimawa ba, Insha Allahul Azeem.


_ Abbakar Ibraheem Kudan

   17122020

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post