Hannunka mai sanda !!!


 

Uhm wallahi abin nan yana bani mamaki, wai meye ribarka ko ribarki, meye nasararki ko nasarsrka, idan ka ko kika dauki rubutun wani kayi masa gyara ka saka a matsayin naka, itafa baiwa ta rubutu Allah ne yake badawa, meye abinda zaki karu dashi ko zaka karu dashi idan ka dauki na wani ka saka, aka rika yabonka akai bayan Kai kasan ba naka bane. 


Ni a ganina duk sanda kaga rubutun wani, kuma kaga yayi maka ma'ana kanaso kayi anfani dashi, to bana tunanin idan ka tambayesa zaka saka ko kayi sharing zaya ce maka meyasa kayi, Amma wai sai wani ya wahalar da kwalwansa yayi rubutu akan wani abu, kuma wai sai wani yazo ya daukesa yayi masa 'yan gyare_gyare, Wai wayo za yayi maka, kawai sai kagansa ya saka, hada saka sunansa akarshe alamar shine yayisa bayan shi yasan ba hakan bane.


Kuma wallahi indai mutum shi yayi rubutu to wallahi duk hikimar da za'ayi Masa wallahi idan ya gansa zaya gane abinsa, haba meye haka wai, don ana kauda kai ba'a magana idan kayi, bafa hakan yake nufin ba'a san abinda kakeyi ba, A'a kawai ana kauda kaine kuma ba'ajin dadin hakan.


Ko Kwanaki naga wani yana magana akan hakan, yayi rubutu wani ya dauka ya saka hada sauya sunansa (shi marubucin ba gaskiya) zuwa na wanda ya dauki rubutun, meye ribar hakan wai, meye ribar??, kowa fa yanada irin baiwar da Allah ya bashi, kayi anfani da naka baiwar mana, basai ka dauki na wani ba, haba wallahi abin yana bani haushi.


Kar kuyi tunanin ni akayiwa hakan, ni har yanzu bankai wannan matakin ba, amma naga anayiwa mutane da dama hakan, kuma basajin Dadi wallahi, ya kamata mu gyara wallahi. Allah ya bamu ikon gyarawa baki daya, afuwan nasiha ce kuma ita kuma tana anfanar mumini ne. 


✍️ zarah A zamsarf

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post