SHIN, WAI DA GASKE NE SHAIDAN NA TSORON UMAR BN KHADDAB ???
Shin, wai da gaske ne Shaidan na tsoron Umar Bn Khaddab ??
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
TAMBAYAR DA MALAMIN SUNNAH YA KASA AMSAWA KENAN
Yana daga cikin karin magana da hausawa ke yi wai, " KOMAI QARFIN TUSA BA TA HURA WUTA ", ko kuma inda suke cewa, " QARYA FURE TAKE BA TA 'YA'YA ."
Da gaske hakane, da mutum zai tattara qirare (fire wood) ya zuba musu garwashin wuta sannan ya shekara yana hurata da tusa ba zai samar da wuta ba sai dai ta hanyar iskar da Allah ya horeta don amfani ga halittunSa, ko kuma wacce mutum ya samar da ita ta hanyar 'yar wata dabara tasa (artificial).
Ita qarya idan aka qirqireta takan bada sha'awa ga wasu har ma kaga suna qoqarin yada ta bisa rashin sani, sai dai da shike ba ta 'ya'ya ba za ta haifar abinda zai amfanar da masu yinta ko jinta ba.
Yana daga cikin qarerayin da aka qirqiro su don nemawa Umar wata falala wacce tafi ta Manzon Allah (S. A. W. W) cewa wai Shaidan na tsoronsa, ko da hangensa yayi a hanya sai ya canza tasa hanyar don kada su hadu.
Shi kuwa Annabi (S. A. W. W) suka ce yana da Shaidan wanda ke zo masa, sai dai ba ya nasara ne a kansa domin wai an cire rabo Shaidan daga zuciyarsa. Shi kuwa Umar wanda ba a cire rabon Shaidan din daga zuciyarsa ba amma a hakan yana tsoronsa ta yadda ko kusantarsa ba ya iya yi.
Ni kuma dana karanta Alqur'ani sai naci karo da wata aya da ke cewa,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
" إِنَّ ٱلَّذِينَ تَوَلَّوۡاْ مِنكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡتَقَى ٱلۡجَمۡعَانِ إِنَّمَا ٱسۡتَزَلَّهُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ بِبَعۡضِ مَا كَسَبُواْۖ وَلَقَدۡ عَفَا ٱللَّهُ عَنۡهُمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ حَلِيمٞ ." ٥٥١
" LALLE WADANNAN DA SUKA JUYA DAGA CIKINKU RANAR HADUWAR JAMA'A BIYU (musulmi da kafirai) , ABIN SANI KAWAI SHAIDAN NE YA LALLABAR DASU SAKAMAKON SASHEN ABINDA SUKA AIKATA (na sabawa Ma'aiki), SAI DAI KUMA ALLAH YAYI MUSU AFUWA , LALLE ALLAH MAI YAFIYA NE MAI JIN QAI. "
(NISA'I:155)
To, abinda ya tabbata cikin tarihi shine, lalle Umar Bn Khaddab na cikin wadanda suka gudu a wannan yaqi na Uhudu sakamakon shafar da Shaidan yayi musu. Shi kuwa Manzon Allah (S. A. W. W) ya tsaya qyam tare da wasu tsiraru ba tare da juya baya ba.
Tambaya anan ita ce, ina tsoron da Shaidan ke yiwa Umar kenan tunda har ya shiga cikin zuciyarsa ya riya masa cewa ya gudu ya tsira da ransa ko da kuwa Annabi (S. A. W. W) zai rasa ransa ta dalilin haka ?
Sunce wai Annabi (S. A. W. W) yayi umarni da hada qafafu cikin sahu yayin sallah wai saboda yana ganin Shaidan na ratsawa ta tsakaninsu don rarraba zukatansu. Shine wani malami daga malaman Shi'ah ke tambayar wani malamin Sunnah da yake tabbatar da wannan magana.
MALAMIN SHI'AH :- Kunce wai duk inda Shaidan ya hangi Umar sai ya canza hanya?
MALAMIN SUNNAH :- Riwaya ta inganta kan haka.
MALAMIN SHI'AH :- Kana nufin Umar ba ya zuwa masallaci sallar jam'i kenan tunda har Shaidan na shiga yana rarratsa tsakanin sahu ?
MALAMIN SUNNAH :- Yana zuwa mana.
MALAMIN SHI'AH :- Idan kace yana zuwa kana qaryata maganar Annabi (S. A. W. W) kenan da yace Shaidan na shiga masallaci tunda kunce Shaidan ba ya hada hanya da shi ko kuma ya gaskiyar maganar take ?
MALAMIN SUNNAH :- Shiru !
MALAMIN SHI'AH :- Idan kuma Umar ba ya zuwa masallaci ne yasa Shaidan ke samun damar shiga masallaci, to, meye matsayin wanda ke qin zuwa masallaci don kada yayi sallah a bayan Annabi (S. A. W. W) ?
MALAMIN SUNNAH :- Shiru !!!
Daga nan malamin Shi'ar ya taqaita tambayoyin gare shi. Shi kuma har yanzu bai sami ikon bada amsar wadannan tambayoyi ba.
KO AKWAI WANDA ZAI TAIMAKA MASA WAJEN AMSA WADANNAN TAMBAYOYI ?
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
17Th December, 2020/ 2nd Jimada-Ulah, 1442.