KU TASHI KU FARKA DIYAN AREWA KUSAN BARCI AIKIN KAWAI NE.


 

(Ko ni Musa da barci nakeyi da tuni nasan an haye ni)


Dazu na gama jin rahoto daga BBC Hausa shirin safe na karfe 6:30 zuwa 7:00, inda aka bayyana cewa jahohin arewacin arewa sun rufe makarantun su na boko, inda katsina da zamfara suka rufe saboda harkar tsaro, kaduna da jigawa suka rufe wai saboda corona, ita kuma jahar Kano bata fadi dalilin rufewar ba.


Yan arewa idan kuka lura wasa-wasa boko haram tana tasiri akan yunkurinta na hana karatun Boko, tunda gaya saboda su an rufe makarantu, kuma dama gaya kididdiga ta nuna cewa yankin arewa shine koma baya a harkar ilimin zamani. Wannan rufe makarantu ya karawa Boko Haram kuzari na ganin sunci nasara, to wallahi banan zasu tsaya ba wani abin Kuma zasu nufa shima su durkusar dashi, kamar asibiti, ko kasuwanci, ko ofisoshin gwamnati. Da sannu sai a kai mu kasa warwas.


Da wannan nake kira ga shugabannin siyasa, gargajiya, addini, kungiyoyi, da sauran jama'a su farka daga barcin da sukeyi don ganin kun ceci rayuwar diyanku da jikokin ku.


Musa Ibrahim Daura

16-12-2020

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post