Meya faru 12 zuwa 14 ga watan Disamba 2015 ?


 

Khadija lawan daura ✍️


Dukkanmu mun ji cewa a ranar Alhamis, 28 ga Safar 1437, dai-dai da 10-12-2015 bayan kammala zaman juyayin wafatin Manzon Allah (s) Shakh Zakzaky ya bayarda sanarwa taron saka tutar maulud Wanda yache za'a gudanar da yammachin ranar Assabar 1 rabi'u Awwal 1437 12-12-2015 


Da misalin karfe 12:15 na ranar Asabar din, wata babban motar Sojoji ta zo ta sauke wasu dandazon kuratan sojoji dauke da bindigu, tare da akwatunan harsashi, a daidai gaban Husainiyyah Bakiyyatullah. Don haka abin da ya yi matukar ba 'yan'uwan da ke wajen mamaki.


An yi kokarin tuntubar su dalilin kawo su gaban Husainiyyah a daidai wannan lokacin, amma sai suka fara harbi a sama. Daga baya sai suka fara kewaye wajen suna harbi, yayin da 'yan'uwa suka bukace su, su matsa daga gaban Husainiyya.


Bayan kamar awa guda da faruwar haka, misalin karfe 1:00 na rana, sai ga tawagar Janar Tukur Yusuf Buratai ta biyo ta wajen Husainiyyar da sunan wucewa. Kai ka ce tawagar ta Shugaban rundunar sojojin Nijeriya ba ta san abin da ya faru a wannan wajen kimamin awa guda da ya gabata ba, wanda ka'idar tsaro zai tilasta masu barin bin hanyar, su koma su bi inda babu kowane irin barazana.


A yayin da wasu 'yan'uwa suka tunkare su don su ji ko da me suka sake dawowa wajen? Sai wasu jami'an tsaro a cikin rigar 'yan'uwa Musulmi (kamar yadda Shugaban DSS na Zariya ya bayyana a gaban JCI cewa akwai mutanensu a cikin 'yan'uwa a wannan ranar a Husainiyyar) suka rika ihu, tare da daddaga sanduna. Nan take sojojin suka bude wuta kan mai uwa-da-wabi.



Bayan bude wutar, tawagar ta Buratai ta wuce, sai wadancan kuratan sojojin da aka kawo da farko suka ci gaba da kewaye Husainiyyah, aka rika karo masu karfi. A yayin da suka bi suka kwashe gawawwakin wadanda suka harba, suka tafi da su barikinsu tun a wannan lokacin.


Duk da wannan abin da ya faru a zahiri, cewa Sojoji sun kawo mana hari ne, amma a shirin rana na BBC a wannan ranar, sai ga hirar Kakakin rundunar soja na wancan lokacin, S.U Kukasheka, inda yake bayyana cewa, wai an yi kwanton-bauna ga Shugaban rundunar sojoji ne, har ma ya tsallake rijiya da baya. 


Kamar yadda duk muka gani cikin cikakken bidiyon wannan harin da Harka Musulunci ta saki daga baya, Soja sun ci gaba da kewaye Husainiyyah, tare da harbin duk wanda suka samu a kewayenta, har zuwa karfe 5:00na yamma, lokacin da Gwamnan Kaduna, Nasiru Ahmad El-Rufa’i ya zo wajen. Bayan magana da ya yi da Jagororin Sojin, sai ya yi gaba. Wucewarsa ke da wuya suka kara tsananta harbe-harbe a Husainiyyar, tare da yunkurin shiganta ta kowane hali.


An ce Elrufai ya kira su Malam (H) a ranar da yamma kafin ya zo Husainiyya wajen Sojojin, da ya kira, ya gabatar da kansa ga Malam, sannan ya masa magana a kan cewa ya ji wani abu na faruwa a Zariya. 


Malam ya bashi amsa da cewa muna da taro ne na saka Tuta a Husainiyya, kuma bikin ba zai wuce minti 30 ba, daga 5 zuwa 6 na yamma an gama. Amma yanzu muna da labarin Sojoji sun zo gaban Husainiyya, sun kewarka ta, kuma har ma sun harbi yan uwa da dama, sun sace wasu bayan sun harbe su sun ji musu rauni, sun tafi da su.


Elrufai ya cewa Malam yana hanya zai zo Zariyan, kuma in ya zo zai nemi Malam din. Amma tsinannen mutumin nan da ya zo sai bai kira din ba, bai je ba. Sai aka ga ya je wajen Husainiyya ya yi magana da Sojoji, ya wuce Bariki sannan ya bar garin.



Bayan dawowan su malan daga darur rahma, su Malam (H) suna ta tunanin ko za a samu fita zuwa saka Tutar, don sam ba a yi tsammanin mutanen nan sun shiryawa yin barnar da ya wuce tunani haka ba. 


Amma daga baya aka tabbatar da ba hanyar tafiya zuwa Husainiyya, don haka ba zai yiwu a je ba. Har Magrib ta yi, aka yi Magariba da Isha, aka cigaba da jira.


Waki'ar da ta faro a Husainiyyah da ke PZ da rana, kwatsam karfe 10:30 daidai na dare sai ga Sojoji sun kawo hari gidan Shaikh Zakzaky a Gyallesu, suna zuwa suka fara harbi ba kakkautawa, har suka kunna wuta a wani shago da ke wajen Banaden, wanda suke amfani da wannan hasken wutan suna seta yan uwan da ke kan Layin suna harbewa.


Zuwa karfe 11:30, awa guda kenan, sun harbi yan uwa kusan 40, kuma cikinsu 11 sun yi shahada an iya kawo gawargwakinsu an aje su. 


Zuwa karfe 12 na dare muka gani a 'Internet' ana ta Muzahara a ofishin jakadancin Nijeriya da ke London, na Allah wadai da abin da ke faruwa a Nijeriya na yunkurin kashe Shaikh Zakzaky. 


Anmafi duk abin da ake din nan, da sanin duniya baki daya a kan halin da ake ciki, bai sa jabberan mutanen nan sun janye ba


A daidai wannan lokaci, suna saka Tociloli ne masu haske suna haska tsakiyar Layin, suna ganin Wanda ke gurin su harbeshi.


Ranache da muminae suka dandani jarabawa mafi tsanani,ranan da fajirae maqiya Allah sukayi taron dangi Dan rusa addinin Allah


Rana che da dukkan masoyi zae tausaya Kuma Ranache wadda ko makiyi indae akwae zuchiyar Dan Adamtaka a jikinsa saeya tausayawa wadannan mazlumae.


Rancher wadda ko dabbobi akayiwa abunda akayimana to tabbatar Allah bazae Bari ba saboda ya martaba rae akan komae shi komae Allah Ta'ala yakan iya baka damar wani rae Kuma daya yayi alqawarin da idan aka kashe bazae taba dawowa ba💖😭


Duk Adam Yana yiwa kansa ka'idodin da zae gindaya wa kansa dabba che kadae keyin abunda takeso a lokachin da takeso.


Shuwagabannin Nigeria da sojojin Nigeria sun dawwamar da bakin chikin da tsawon shekara biyar Amma har yanxu akwae hawaye suna zuba a idanunmu sannan zuchiyarmu tana Kuna😭


A ranan ne buhari ya mayarda kananan yara marayu ya mayar da Mata zawarori ya kashe Mata da yara da tsofi wa'eyazubilla a ranan ne aka kashe jariri Wanda idan iyayensa sunyi laefi shi bae aekata komae ba ko a wurin Allah shi mafi soyuwa ne Amma sojojin Nigeria sun harbe💖😭


An Kona Yar uwar Shakh Zakzaky da ranta Tana fadar ku barni na gana da Dan uwana Amma suka banka wuta a dakin da take takone💖😭


Aka karasa kashewa Sayyid Zakxaky yaransa guda 3 a gabansa har gwagwalwar daya ta tarwatse a fuskansa aka harbi Mai dakinsa sannan aka Masa Harbin kisa aka jashi akan gawar yayansa da almajiran sa 💖😭


A karshe dai an kashe Almajiran malan sama da 1000+ Haqiqa buhari yayi ta'addanchin Kuma Allah bazae taba barinsa ba Allah ka gaggauta daukar Mana fansa ka gaggauta saka Mana wutar data ruru a zukatanmu Allah ka dawwamar da ita a zukatansu Azabtarwar da suka Mana Allah ka Azaftasu da wutarka Allah ka gaggauta bayyanar Dan narjees ka bawa sayyid zakxaky lafiya da Mae dakinsa Allah ka karbi shahadar shahidanmu🙏 ilahee

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post