ZariaMassacre: Zazzafar Muzaharar tunawa da Waki'ar Zariya a garin Jos



A safiyar yau Asabar Wanda tayi daidai da 12\12\2020 Muzarar Allah wadai da kisan kiyashi akan Yan uw Musulmi Almajiran Sheikh Zakzaky a Shekarar 2015, Sojin Nigeria marasa rabo karkashin jogorancin Tukur Yusuf burutai (l) Suka afkawa Hussainiyya da gidan Sheikh Zakzaky Suka kashe mutane sama da dubu.


An dakko Muzahar daga daidai Yan Taya aka biyo titin bauchi road aka shigo ta Salisu Adamu sannan aka rufe Muzahar a daidai Kasuwar New Market. 


Malam Abubakar (Dattijo) shine yayi jawabin Rufewa Linda Malam Bala yayi Addu'a. 


Muzarar ta sami cikowar Yan uwa daban daban kuma lallai ta isa inda ake da bukatan ta isa. 


Allah ya gaugauta fito mana da Jagoranmu Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) daga hanun mutane Azzalumai muna fatan Allah ya karbi Shahdar shahidanmu, muma intamu tazo Allah ya karbemu a matsayin Shahidai. 


Daga Almustapha A Abdullahi Jos

Ga wasu hotuna da muka dauki muku



 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post