Mazajenmu, ababen alfaharinmu, farin cikinmu, kuma jigon rayuwarmu !!!


 

Dukkan godiya da yabo su tabbata ga mahaliccin farin ciki, tsira da aminci su kara ninkuwa ga fiyayyen fiyayyayu, abin koyi ga duk wata halitta, mukaddimu sidikir rahman, Muhammad bn Abdallah, da alhalin gidansa da sahabbansa na gartattu.



Hakika Allah ya sallada jin Dadi da farin cikin rayuwar mutane mafiya rauni a karkashin masu karfi, ya kuma umarci hada auren mai raunin tunani da mafificin hakan, tabbas mata abin tausayawa ne ta kowane fuska, duba da yanda halittarsu ma ta samo asali, hakan ne yasa Allah ya hada zaman takewarmu ta zama tsakanin mai rauni da mai karfi.



Mazajenmu, farin cikinmu abin alfaharinmu, tabbas ku jigo ne acikin rayuwarmu, duk abinda zamuyi munada bukatawa a gareku, mun kasance masu rauni ta kowane fuska, tun daga kan tunani har a ayyukanmu, Allah ya hadamu ne don ku kasance mana gata, rahama, farin ciki, da jin dadi na duniya da lahira.


Su din abin girmamawa ne, abin darajtawa ne, abin ayiwa biyayyane akan duk dokokin da Allah ya gindaya mana game dasu, sudin wani mahadi ne na rayuwarmu, farin ciki, da haske acikin rayuwarmu, gaesuwa ga mazajenmu farin cikinmu iyayenmu iyayen ya'yanmu, bangayenmu abin jinginarmu.


Ya Allah ka sanya haskenka acikin kirazan ma'abota tausayi, ka sanya rahamarka ga ruhukan masu jin kai, ka kasance da masu darajtawa da girmamawa, ka biyawa masu dauke nauyi da kyautatawa, ka sakasu a aljannarka mafi girma, wa'yanda ke kula da tausayawa masu rauni a tunani da ayyuka (mata), ya Allah ka yarda dasu ka kasance mana a tare dasu a kowane hali, ka cika masu burikansu na alkhaeri, ka iyawa damuwarsu darajar mafi daraja da girma.


Dole mu yabeku mu gode maku, mu sara maku, mu jinjina maku, Allah ya cigaba da baku damar sauke hakkokinmu dake kanku, muna sonku muna son farin cikinku, fatan kuma zaku kasance rahama, kuma hanyarmu ta zuwa ga Allah mai girma cikin aminci.


✍️ Zarah A Zamsarf

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post