@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
IDAN KA FARO TA KAN ABUBAKAR SAI IDANUWANKA SUNYI JA
Duk da cewa batun adadin Khalifofin Annabi (S. A. W. W) a bayansa su 12 ne kamar yadda yazo cikin littafan muslimci na Shi'ah da Sunnah, amma hakan bai hana Ahlus-Sunnah rufe ido su qirqiro wasu na bogi ba.
Idan ka kasa musulmi kashi 100, to, daga cikinsu za ka sami kashi 85 sun tafi akan 4 ne sakamakon cin amanar da wasu malaman Sunnah su kayi musu ta hanyar boye gaskiyar abinda Annabi (S. A. W. W) ya fada.
Babu mamaki har kai ma mai karanta wannan saqo 4 ka sani ba ka san cewa 12 bane Annabi (S. A. W. W) ya bar mana wadanda za su jagorance mu cikin rayuwarmu.
Idan muka koma cikin Qur'ani inda Allah (T) ke cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
" وَلَقَدۡ أَخَذَ ٱللَّهُ مِيثَٰقَ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ وَبَعَثۡنَا مِنۡهُمُ ٱثۡنَيۡ عَشَرَ نَقِيبٗاۖ وَقَالَ ٱللَّهُ إِنِّي مَعَكُمۡۖ ..........."
" KUMA HAQIQA ALLAH YA RIQI ALQAWARIN BANU ISRA'ILA, SAI MUKA TAYAR DA WAKILAI GOMA SHA BIYU (12) DAGA CIKINSU, KUMA ALLAH YACE, " LALLE INA TARE DA KU.......
(MA'IDA:12)
Wadannan wakilai 12 an zabe su ne domin su wakilci Banu Isra'ila wajen daukar alqawari ga Musa (A. S) kan cewa za su bi Allah.
Ibn Katheer ya kawo riwayoyi masu yawa qarqashin Tafsirin wannan aya, ga wasu daga cikinsu :-
(1)- Imamu Ahmad yace, Hassan Bn Musa ya bamu labari, Hammad Bn Zaid ya bamu labari daga Mujalidi, daga Sha'abiy daga Masruq yace, " Mun kasance zaune a wajen Abdullahi Bn Mas'ud (R. A) yana karanta mana Alqur'ani, sai wani mutum yace masa, " Yaa baban Abdurrahman ! Shin, kun tambayi Annabi (S. A. W. W) nawa ne za su jagoranci wannan al'umma daga Khalifofi ?" Sai Abdullahi yace,
" TUNDA NAZO IRAQI BAN SAMI WANDA YAYI MIN WANNAN TAMBAYA BA GABANINKA. " Sa'an nan yace, " NA'AM, HAQIQA MUN TAMBAYI MANZON ALLAH (S. A. W. W) SAI YACE,
" SU GOMA SHA BIYU (12) NE KAMAR ADADIN WAKILAN BANU ISRA'ILA ."
(Musnad Ahmad, J:1, Sh:398, 406).
(2)- Jabir Bn Samrata yace, na ji Manzon Allah (S. A. W. W) na cewa;
" AL'AMARIN MUTANE BA ZAI GUSHE BA (sasakai) BA TARE DA MUTANE 12 SUN JAGORANCE SU BA ."
Sa'an nan Annabi (S. A. W. W) yayi wata magana wacce ta kubuce min, sai yayi tambaya cewa menene Annabi (S. A. W. W) ya fada ? Yace,
" DUKKAN SU DAGA QURAISHAWA NE ."
- (Muslim, J:6, sh :3)
- (Musnad Ahmad, J:5, SH:99,100).
ABINDA BUKHARI YA KAWO
(1)- Abu Yamani ya bamu labari, Shu'aibu ya bamu labari....... sai Mu'awiyyah ya fusata, sa'an nan ya miqe yayi yabo ga Allah da irin abinda ya dace da shi, sa'an nan yace,
" Bayan haka, lalle labari ya iso gare ni cewa lalle wani mutum daga cikinku yana bada labari irin labarin da ba ya cikin littafin Allah, kuma ba a riwaito daga Manzon Allah (S. A. W. W) ba, to, wadannan sune jahilanku ! Na hane ku datatsuniyoyin da ke halakar da masu shi, domin ni na ji Manzon Allah (S. A. W. W) yana cewa,
" LALLE WANNAN AL'AMARI (KHALIFANCI) NA QURAISHAWA NE, BABU WANDA ZAI TUNKUDE SHI DAGA GARE SU FACE ALLAH YA KIFAR DA SHI TA FUSKARSA KO DA KUWA YANA TSAYAR DA ADDINI ."
(2)- Baban Waleed ya bamu labari, Aseem Bn Muhammad ya bamu labari yace; " Na ji babana daga Ibn Umar (R. A), daga Annabi (S. A. W. W) yace,
" WANNAN AL'AMARI (KHALIFANCI) BA ZAI TABA GUSHEWA CIKIN QURAISHAWA BA MATUQAR MUTUM BIYU DAGA CIKINSU ZA SU RAGE (a duniya) ."
(Sahihul-Bukhari, kitabi na 61,(Kitabun Manaaqeeb), babi na 2 (babun manaaqebun-Quraish), hadisi me lamba 3500,3501).
Duk da cewa wasu sun ce wai Abubakar Baquraishe ne, amma ittifaqan Usman Bn Affan daga Banu Umayyah yake.
IDAN KA FARO TA KAN ABUBAKAR SAI IDANUWANKA SUN YI JA A
Uhmm, Ibn Katheer yayi qoqarin kawo wannan adadi 12, amma da ya faro ta kan Abubakar sai da idanuwansa su kayi jaa !
Ga abinda ya kawo
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
" Ma'anar wannan hadisi bushara ce ta samuwar Khalifofin 12 salihai, za su tsayar da gaskiya kuma suyi adalci a cikinsa. Sai dai wannan jerin da bibiyar kwanakinsu bai lazimta ba. A'a, haqiqa mun sami 4 a Jere, sune :-
Abubakar,
Umar,
Usman da
Aliyu (R. A).
Kuma daga cikinsu akwai Umar Bn Abdul-Azeez wanda babu kokonto kansa wajen A'imma, da kuma sashen Banu Abbas.
Qiyama ba za ta tsaya ba har sai wilayarsu ta samu babu makawa !
Abinda kuma yafi bayyana shine, daga cikinsu akwai Mahdi wanda akayi bushara da shi cikin hadisai da aka riwaito da ambatonsa. Kuma an ambaci cewa sunansa zai zo daidai da sunan Annabi (S. A. W. W) da suna babansa, zai cika qasa da adalci da daidaito kamar yadda ta cika da zalunci da mutunta.
Amma fa ba ana nufin MUNTAZAR wanda rafidhawa ke wahami da samuwarsa ba, sa'an nan suka kururuta shi cikin larduna, domin shi (A. F) ba shi da tabbas, kuma ma gaba daya babu shi......
(Tafsir Ibn Katheer, J:2, Sh:39)
Yanzu mun ji 6, ina sauran 6 da ka gagara kawo su ?
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
21st December, 2020/ 7th Jimada-Ulah, 1442.
Kalmar ka ta karshe akan muntazar?
ReplyDelete