Idan ka yafewa mutum laifin da yayi ma na farko, ya shafi wanda zai qara yima a gaba ??


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


HUKUNCIN DA HAR YANZU MAFI YAWAN MALAMAI BA SU SAN SHI BA 


Yana daga cikin siffofin Allah (T) cewa Shi mai yafiya ne mai gafara (AL-AFUUWU AL-GAFUURU), kuma shine (T) ya sanar damu cewar yana gafartawa kan dukkan wasu laifuffukan da za mu aikata matuqar dai ba shirka bane. Kuma ko da shirkar ce ma yana gafartawa wanda ya tuba kafin mutuwarsa. 


Ita kuwa biyyayya ga Manzon Allah (S. A. W. W) wajibi ce kan dukkan mumini, duk wanda ya saba umarnin Manzo (S. A. W. W) Allah ya sabawa, kamar yadda biyayya gare shi ta kasance biyayya ga Allah. 


Allah (S. W. A) na cewa, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


" يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَ وَأُوْلِي ٱلۡأَمۡرِ مِنكُمۡۖ.................


" YAA KU WADANDA SU KAYI IMANI ! KUYI 'DA'A GA ALLAH KUMA KUYI 'DA'A GA MANZO DA MA'ABOTA AL'AMRA (shuganni) DAGA CIKINKU....... "


                  (NISA'I:59)


Saboda haka ne Manzon Allah (S. A. W. W) ke cewa, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


" DUK WANDA YAYI MIN BIYAYYA HAQIQA YA YIWA ALLAH, KUMA WANDA YA SABA MIN HAQIQA YA SABAWA ALLAH, WANDA YA YIWA SHUGABA BIYAYYA HAQIQA NI YA YIWA, WANDA KUMA YA SABA MASA TO, NI YA SABAWA ."


      (Bukhairi :7137)


Annabi (S. A. W. W) yayi umarni kan cewa abi Imam Ali (A. S) a matsayin jagora bayansa, Sannan ya qara umartar Sahabbai cewa su tafi yaqi qarqashin Usamatu Bn Zaid (R. A), amma sai suka qi yin biyayya gare Shi (S. A. W. W) bisa hujjar cewa wai su qananan yara ne a kansu, sun manta da cewa yaran ne suka taka rawar gani cikin dukkan yaqoqin da Annabi (S. A. W. W) yayi don daukaka addinin muslimci. 


Sannan kuma ya qara umartarsu da su ba shi abin rubutu ya rubuta musu abinda matuqar sunyi riqo da shi ba za su bata ba a bayansa, amma suka nuna cewa ba sa buqata, wai littafin Allah ma ya ishe su. 


      (Bukhairi :5669)


Idan kuma kace wannan saba umarnin Manzo (S. A. W. W) ne wanda hakan kan iya kai mutum wuta sai ka ji suna kafa maka hujja da cewa, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


" لَّقَد تَّابَ ٱللَّهُ عَلَى ٱلنَّبِيِّ وَٱلۡمُهَٰجِرِينَ وَٱلۡأَنصَارِ ٱلَّذِينَ ٱتَّبَعُوهُ فِي سَاعَةِ ٱلۡعُسۡرَةِ مِنۢ بَعۡدِ مَا كَادَ يَزِيغُ قُلُوبُ فَرِيقٖ مِّنۡهُمۡ ثُمَّ تَابَ عَلَيۡهِمۡۚ إِنَّهُۥ بِهِمۡ رَءُوفٞ رَّحِيمٞ ٧١١ ."


" HAQIQA ALLAH YA KARBI TUBA AKAN ANNABI DA MUHAJIRUUN DA ANSAR WADANDA SUKA BI SHI A LOKACI MAI TSANANI DAGA BAYAN SUNYI KUSA DA ZUKATAN WASUNSU SU KARKATA, SA'AN NAN YA KARBI TUBAR SU, LALLE SHI GAME DASU MAI TAUSAYI NE MAI JIN QAI ."


           (TAUBA :117)


Wannan abu kuwa ya faru ne sakamakon qin fitar wasu zuwa yaqin Tabuka ba tare da wani uzuri ko lalura ba, sai dai don tsoron mutuwa da kuma sabawa Ma'aiki (S. A. W. W). Amma bayan horon da akayi musu sai kuma Allah ya karbi tubar su na wannan sabawar da suka yi. 


Da wannan hujja wasu ke kafawa cewa wai ko ma me za suyi Allah ya riga ya yafe musu. 


Shine muke tambaya da cewa, ko da sun qara aikata wani laifi na saba umarnin Annabi (S. A. W. W) a bayan wancan za su fada cikin tubar farko ?


To, ku san abinda ba ku sani ba, Allah (T) na cewa, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼



" فَلَا وَرَبِّكَ لَا يُؤۡمِنُونَ حَتَّىٰ يُحَكِّمُوكَ فِيمَا شَجَرَ بَيۡنَهُمۡ ثُمَّ لَا يَجِدُواْ فِيٓ أَنفُسِهِمۡ حَرَجٗا مِّمَّا قَضَيۡتَ وَيُسَلِّمُواْ تَسۡلِيمٗا ." ٥٦ 


" NA RANTSE DA UBANGIJINKA ! BA ZA SUYI IMANI BA HAR SAI KA KASANCE KAI KAKE YIN HUKUNCI CIKIN ABINDA YA GUDANA (faru) A TSAKANINSU, SA'AN NAN BA SU JI WANI QUNCI CIKIN ZUCIYARSU NA DAGA ABINDA KA HUKUNTA BA, KUMA SUKA SALLAMA DUKKAN SALLAMAWA ."


             (NISA'I :65)


Amma sanin kowa ne a qarshen rayuwar Annabi (S. A. W. W) yayi hukunci da umarni amma sun qi yin biyayya gare shi, sannan kuma ba a qara samun wata aya ta sauko kan karbar tubarsu na wannan qin biyayyar ba .


Yanzu wanda ya aikata haka za ka kira shi mai imani ?


Hukuncin da ka samu shine hukuncin wadanda su kayi biyayya a yanzu ga wadanda ba sune jagororin muslimci ba .


Daga wakilanmu na Bauchi. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 


       (08137925034)


22nd December, 2020/ 8th Jimada-Ulah, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post