@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
ABUBAKAR BAI YI HIJRA TARE DA ANNABI (S. A. W. W) BA
Yana daga cikin mafi girman cin amanar muslimci qirqiro qarerayi a cusa su cikin littafan muslimci don cimma wani muradi na qashin kai.
Wadanda ba musulmi ba suna karanta littattafanmu na muslimci sannan suna ganin irin wadannan qarerayi wanda hakan ya taimaka wajen qyamatar addininmu bisa hujjar an gauraya shi da qarerayi.
Daga cikin qarerayin an qirqiro wasu falaloli na qarya aka Qaqabawa wasu don fifita su akan wadanda suka fi su, hakan kuwa abin kunya ne cikin addinin da ake iqirarinsa a matsayin mafificin addini .
Muslimci shine mafificin addini kuma shi yafi cancanta da a sami gaskiyar magana a cikinsa ko da kuwa hakan zai baqantawa wasu rai ko ya fattanawa wasu .
ABUBAKAR BAI YI HIJRA TARE DA ANNABI (S. A. W. W) BA
Abinda malaman tafsirai suka kakkawo cikin tafsiransu game da ayar nan dake cewa,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
" إِلَّا تَنصُرُوهُ فَقَدۡ نَصَرَهُ ٱللَّهُ إِذۡ أَخۡرَجَهُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ ثَانِيَ ٱثۡنَيۡنِ إِذۡ هُمَا فِي ٱلۡغَارِ إِذۡ يَقُولُ لِصَٰحِبِهِۦ لَا تَحۡزَنۡ إِنَّ ٱللَّهَ مَعَنَاۖ ..........."
" IDAN BA KU TAIMAKE SHI BA, HAQIQA ALLAH YA TAIMAKE SHI YAYIN DA KAFIRAI SUKA FITAR DA SHI YANA NA BIYUN BIYU, YAYIN DA SUKE CIKIN KOGO. YAYIN DA YAKE CEWA ABOKINSA KADA KAYI BAQIN CIKI, LALLE ALLAH NA TARE DAMU........ "
(TAUBA :40)
Sai suka ce ai wannan abokin nasa wanda su kayi Hijra tare har suka shiga cikin kogon Thaur shine Abubakar. Kuma sun kawo hakan ne don su samar masa wani matsayi na musamman (special). Sun yi nasarar hakan kuwa domin cikin falalin da suka kawo nasa babu wanda ya fi wannan girma kuma ya fantsama cikin dukkan bangarori na muslimci ba tare da sun san qaryar bace.
Allah bai kama sunansa ba cikin wannan aya ballantana kace ana qaryata ta, sai dai kawai malamai suka qirqiro sunansa.
HUJJA KAN WANNAN MAGANA
(1)- Bukhari ya riwaito cewa, Ibrahim Bn Munziri ya bamu labari yace : Anas Bn Iyadh ya bamu labari daga Ubaidullahi, daga Nafi'i, daga Abdullahi Bn Umar yace :
" YAYIN DA MASU HIJRA NA FARKO SUKA ISO WANI GURI A QUBA'I WATA JAMA'A CE KAFIN ISOWAR MANZON ALLAH (S. A. W. W), KUMA SALEEM BARARREN BAWAN BABAN HUZAIFATA YA KASANCE YANA JAGORANTASU (sallah) DOMIN SHI YA FI SU SANIN QUR'ANI ."
(Sahihul-Bukhari, kitabi na 10 (KITABUL-AZAAN), babi na 54 (BABUN IMAMATIL ABDI WAL-MAULAH) hadisi mai lamba 692).
Idan kace a ina aka nuna cewa Abubakar na cikinsu? Sai nace maka ai Bukharin yace don ganin cigaban wannan hadisi a duba hadisi mai lamba 7175.
(2)- Bukhairi yace, Usman Bn Salih ya bamu labari, Abdullahi Bn Wahbin ya bamu labari, Ibn Juraij ya bamu labari cewa lalle Nafi'i ya ba shi labari cewa lalle Ibn Umar ya ba shi labari cewa : " SALEEM BARARREN BAWAN BABAN HUZAIFATA YA KASANCE YANA JAGORANTAR MASU HIJRA NA FARKO DA SAHABBAN ANNABI (S. A. W. W) CIKIN MASALLACIN QUBA'I, KUMA A CIKINSU AKWAI ABUBAKAR DA UMAR DA ABU SALAMATA DA ZAID DA AMEER BN RABEE'ATA ."
(Sahihul-Bukhari, kitabi na 94 (KITABUL-AHKAAM), babi na 25 (BABUN ISTIQDHA'IL-MAWAALIY WAS-TI'IMALIHIM), hadisi mai lamba 7175).
Wannan hadisi na tabbatar mana ne da cewa ashe Abubakar ya riqa yayi Hijra zuwa Madinah kafin Allah ya yiwa Annabi (S. A. W. W) umarnin barin garin Makkah.
Idan kace hakan ya faru ne bayan isowar Annabi (S. A. W. W) Madinah, sai nace maka ai cikin hadisi na 692 Ibn Umar yace hakan ya faru ne kafin isowar Annabi (S. A. W. W) Madinah.
Sai kuma na qara da yima tambaya da cewa, shin, bayan isowar Annabi (S. A. W. W) garin Madinah ya sanya masallatai biyu (2) ne wanda shi yake jagorantar wasu a daya (1) Saleem ma ke jagoranci cikin dayan ?
Idan kuma kace lalle Abubakar tare da Annabi (S. A. W. W) su kayi Hijra sai nace maka, shin, komawa garin Makkah yayi bayan Hijrar farkon da yayi ya sami Annabi (S. A. W. W) suka taho tare ko kuma qarya ne ba ya cikin masu Hijrar farko kamar yadda Ibn Umar ya fada ?
Uhmm, ashe ma akwai wanda ya fi su ilimin Qur'ani har ya riqa jagorantarsu sallah amma ku kayi qarya da cewa wai babu wanda ya taba jagorantar Abubakar koma bayan Annabi (S. A. W. W).
YAA ALLAH ! KA QARA TONA ASIRIN MAQARYATA KA BAYYANAR DA GASKIYA GA MASU NEMANTA DA SON BIN TA.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08126385470)
20th December, 2020/ 6th Jimada-Ulah, 1442.