Muna kira da Malaman Musulunci da Sarakuna da yan'siyasa da suji tsoron Allah su komo wa gaskiya!
A Nijeriya angwada siyasa da babu Addini an gwada PDP da APC duk sun kai mutane zuwa ga halaka da musiba da kashe kashen rayuka ga fatara da yun'wa na karuwa !Komi ya tabar bare !! Sakamakon an bar Addini !Idan da ance wancan jam'iyar Kafiraine basa Salla to yanzu angwada jam'iyar masu Sallah !harma ance babu mai gaskiya kamar shugabanta wasu ma sunce waliyi ne !!? To, Yanzu me za'ace wa mutane ?!!
Yanzu ba abinda ya rage agwada sai Musulunci ! Don haka muna fatan Malamai da sarakuna da yan'siyasa da kuma sauran talakawa za a komo ga Musulunci a rayuwar mu da siyasa da Gwamnatance !
Idan Malamai da yan'siyasa zasu sa mutane su bada ransu da dukiyar su da lokacin su don damokiradiya ! To, Lallai babu wani uzuri da Malamai zasu bayar wanda zai sa baza ayi wa Musulunci irin wannan sadaukarwan ba ! ? Sai dai in Musulunci bashi da gata a wurin Musulmi ko kuma ba'a yarda shine hanyar tsira ba !!!
Yanzu zamu sa ido muga wani kamfen na siyasa Malamai za suyi wa mutane a Masallatai ! !
#FreeZakzaky