Kogin So, fadawa ba wahala, fitowa lafiya sai mai sa'a... Fita ta goma (10)


  Rbtwa: J. I. R


Ahmad ya shiga halin, Allah ga ni gareka. Damuwa ta samu mazauni a Zuciyarsa yana tunanin shikenan abun da ya saba da shi ya guje shi, haka nan dai ya shiga damuwa sosai har ya sanya a ransa Zainab ta yi masa halin wasu matan.


Wata rana kwatsam! Sai ga labari ya iso ma Ahmad kan cewa, "Zainab ai ta samu wani Alhaji mai kudi, sunansa Hudu", Ahmad da jin haka saboda tsananin bakin ciki da cin amanar da Zainab ta masa ya yanke jiki ya fadi. Nan take a daukesa sai a asibiti, a kwantar da shi a dubasa, karshe dai ya samu lafiya bayan ya shafe sati biyu a asibiti. Zainab kowa tana can ko oho! Ba ta ma kawo halin da zai kasance. Bata san labari ya iso masa ba.


Zainab su ci gaba da soyayyarsu da Alhaji Hudu, har a zo soyayyar da Zainab take yiwa alhaji Hudu ya dara nasa. Tana son alhaji Hudu fiye da yanda yake sonta.


Ahmad ya dawo har ya manta ya mayar da komai ba komaiba. Ya barwa Allah ya masa sakayya, ya yi kokari a hankali ya fitar da damuwar da Zainab a baya ta saka masa. Ya zo ma ya ci gaba da harkarsa.


Zainab bayan shafe wata daya a garin kakanta Hadiza, ta dawo gida cikin yanayi na jin dadi. Tana dawowa ta hadu da ummansu, Zainab "Ummah! Sannu umma kai umma na yi kewarki" Mamansu "Kai Zainab sannu dai ke ce ki yi kiba ki yi fari, amma kaka ta kula dake sosai wanan tafiyar dayake kin dade ba ke jeba". Haka dai su gama gaisawa. Ta zo ta hadu da kawarta Fatima, Fatima daga ganinta ta dau murmushi "Zainab la sannu kai amma kin kiba ga fari da ki dada, dole ki dade kiqi dawowa, amma kiwon kauye ya amsheki" Zainab: "Uhmm bari kawai Fatima, gobe in na huta akwai labari mu hadu da yamma zan zo gidanku".


Mu hadu a kashi na gaba don jin ya za ta kasance.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post