Ko kun san Al-kabaeer daga cikin laifuffuka ???


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


YADDA YAZO CIKIN TAFSIRUL-QUMMY 


Al-Kaba'eer dai wasu manyan laifuffukan ne wadanda Allah (T) ya hane mu aikata su, kuma yace mana matuqar mun qaurace musu zai gafarta mana sauran qananan laifuffukan da muke aikatawa bisa irin rauni (weaknesses) namu. 


Na'am, a wata riwaya an kawo su da yawa, amma yanzu za mu kawo yadda Sheikh Abbasul-Qummy ne ya kawo cikin Tafsir nasa kan ayar da ke cewa ,


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼



2- فس، تفسير القمي‏



" إِنْ تَجْتَنِبُوا كَبائِرَ ما تُنْهَوْنَ عَنْهُ‏......"


" IDAN KUKA NISANCI MANYAN LAIFUFFUKA DA MUKA HANE KU A KANSU..... "


 قَالَ هِيَ سَبْعَةٌ الْكُفْرُ وَ قَتْلُ النَّفْسِ وَ عُقُوقُ الْوَالِدَيْنِ وَ أَكْلُ مَالِ الْيَتِيمِ وَ أَكْلُ الرِّبَا وَ الْفِرَارُ مِنَ الزَّحْفِ وَ التَّعَرُّبُ بَعْدَ الْهِجْرَةِ وَ كُلُّ مَا وَعَدَ اللَّهُ فِي الْقُرْآنِ عَلَيْهِ النَّارَ مِنَ الْكَبَائِرِ[7].



Yace, su bakwai (7) ne :-


(1)- KAFIRCI, 


(2)- DA KASHE RAI, 


(3)- DA SABAWA MAHAIFA, 


(4)- DA CIN DUKIYAR MARAYU, 


(5)- DA CIN RIBA, 


(6)- DA GUDU A FAGEN YAQI, 


(7)- DA KUMA YIN RIDDAH BAYAN HIJRA. DA DAI DUK ABINDA ALLAH YAYI ALQAWARIN WUTA A KANSA NA DAGA CIKIN AL-KABA'EER ."


(2) تفسير القمّيّ ص 124 و 125.


Saboda haka sai mu nisanci aikata irin wadannan miyagun ayyuka don neman samun yardar Allah. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 


        (08137925034)


19th December, 2020/ 5th Jimada-Ulah, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post