@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
HUKUNCIN MAHAUKACIYAR DA TA SHA GIYA
Za ka iya fahintar cewa ashe karatu ba komai bane in dai za ayi shi ba tare da nazari ko tadabburinsa ba, hakama saurare in ba a hada shi da fahinta ba.
Sau da yawa mutum zai iya yin karatu ko sauraren wata magana daga bakin wani, amma idan ka nemi sanin wani hukunci cikin karatun nasa ba za ka samu ba, haka ma cikin sauraren nasa ba zai iya qarar da kai komai ba, domin shima bai fahinci abinda ya saurara ba.
Saboda haka duk lokacin da za kari karatu kana fahintar me kake karantawa, ko kuma ka riqa saurare na fahintar maganar da ake fada, ta hanyar hakane za ka iya bayar da shaida ko yin hukunci.
Wani al'amari ya auku zamanin mulkin Umar Bn Khaddab na hukunci, amma sai aka sami matsala cikin hukuncin da ya riqa zartarwa. Hakan kuwa ba zai zama abin mamaki ba don an sami kuskuren hukunci cikin hukunce-hukuncen da mutane ke zartarwa matuqar ba sun sha ruwan ilimin daga mabubbugarsa bane.
Ga wani misali da yazo cikin AL-IKHTISAAS kamar haka,
7- ختص، الإختصاص عَنِ ابْنِ يَزِيدَ عَنِ ابْنِ أَبِي عُمَيْرٍ قَالَ: قَالَ مُؤْمِنُ الطَّاقِ لِأَبِي حَنِيفَةَ فِي كَلَامٍ طَوِيلٍ جَرَى بَيْنَهُمَا إِنَّ عُمَرَ كَانَ لَا يَعْرِفُ أَحْكَامَ الدِّينِ فَإِنَّهُ أُتِيَ بِامْرَأَةٍ حُبْلَى شَهِدُوا عَلَيْهَا بِالْفَاحِشَةِ فَأَمَرَ بِرَجْمِهَا فَقَالَ لَهُ عَلِيٌّ ع إِنْ كَانَ لَكَ السَّبِيلُ عَلَيْهَا فَمَا سَبِيلُكَ عَلَى مَا فِي بَطْنِهَا فَقَالَ لَوْ لَا عَلِيٌّ لَهَلَكَ عُمَرُ وَ أُتِيَ بِمَجْنُونَةٍ قَدْ زَنَتْ فَأَمَرَ بِرَجْمِهَا فَقَالَ لَهُ ع أَ مَا عَلِمْتَ أَنَّ الْقَلَمَ قَدْ رُفِعَ عَنْهَا حَتَّى تَصِحَّ فَقَالَ لَوْ لَا عَلِيٌّ لَهَلَكَ عُمَرُ[11].
Daga Ibn Yazeed, daga Ibn Abiy Umairin yace, Mu'uminu Ad-Daaqi ya kawo daga Abu Haneefata cikin wani zance mai tsaho da ya gudana a tsakaninsu cewa, lalle Umar bai san hukuncin addini ba. Domin kuwa anzo masa da wata mata mai ciki wacce aka yi shaida a kanta da aikata alfasha, sai yayi umarni da a jefe ta. Sai Aliyu (A. S) yace masa;
" IDAN YA KASANCE KANA DA DAMA A KANTA (saboda ta aikata abinda hukunci ya hau kanta), TO, WACCE DAMA KAKE DA ITA KAN ABINDA KE CIKIN CIKINTA ?" Sai yace,
" DA BA DON ALIYU BA DA UMAR YA HALAKA !"
Sannan kuma aka zo da wata mahaukaciya wacce ta aikata zina, sai yayi umarni da a jefe ta. Sai Aliyu (A. S) yace masa;
" AMMA DAI KA SAN CEWA AN 'DAUKE ALQALAMI A KANTA HAR SAI TA SAMI LAFIYA ?" Sai yace,
" DA BA DON ALIYU BA DA UMAR YA HALAKA ."
________________________
(2) الاختصاص: 111، و قد ذكر المؤلّف العلامة تمام الحديث في ج 10 ص 230 من هذه الطبعة باب احتجاجات أصحاب الصادق عليه السلام على المخالفين.
Wannan kuwa qalu-bale ne ga ma'abota neman ilimi ko masu zartar da hukunci, domin gare su ake mayar da al'amari in ana neman sanin hukuncin abubuwa.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
19th December, 2020/ 5th Jimada-Ulah, 1442.