@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
IDAN KA SAMI KANKA CIKIN KASHI NA UKU KA FADA CIKIN AZZALUMAI
Al'ummar Manzon Allah (S. A. W. W) ta kasu gida biyu ne bisa babi na dabi'a ba bisa babi na aqida ba. Azzalumai wadanda suka kangarewa Allah ta kowacce fuska da kuma raunana masu biyayya ga Allah wadanda ake zalunta.
Su wadannan azzalumai sune wadanda suke bijirewa dokar Allah suka bi Shaidan wajen ayyukansu da zantukansu, kuma suke gaba da wadanda suka ce su Allah za su bi a matsayin mai basu doka da oda cikin komai nasu.
Raunana wadanda ake zalunta sune wadanda suka sallama rayuwarsu ga Allah da kuma neman yardarsa, sannan suna qoqarin nunawa mutane cewa Allah ne yafi cancanta a bauta masa da kuma bin dokarsa.
Akan haka suke fuskantar cutarwa da tsangwama daga azzaluman mahukunta masu fifita dokarsu akan ta Allah.
Dole ya kasance kana cikin ajin azzalumai ne masu qoqarin bice hasken Allah (muslimci) a doron qasa, ko kuma ka kasance cikin masu qoqarin dawo da martabar muslimci ta hanyar fitowa ayi magana don hana zalunci da shirka.
Ba zai yiwu ka sami kanka cikin aji na uku ba ('yan ba ruwanmu), wato wanda ba ya goyon baya ko tare da daya cikin ajujuwa biyu (azzalumai ko wadanda ake zalunta).
Irin haka ta faru kan ma'abota kifi (AS-HABUS-SABTI). Allah ya hane su da yin su (fishering) ranar azabar, sai aka sami wasu suna aikatawa, wasu kuma suna yin hani da gargadi ga masu yin wannan aiki da Allah ya hane su, wasu kuma suka tsaya a gefe ba sa aikatawa kuma ba sa yin hani ga masu aikata wannan aiki. Har ma suna zargin masu yin hani da cewa bai kamata su bata lokacinsu suna magana kan abinda kowa yasan laifi ne kuma zai yi hukunci a kansa ba.
Allah (T) ya kawo mana wannan labari kamar haka,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
" وَإِذۡ قَالَتۡ أُمَّةٞ مِّنۡهُمۡ لِمَ تَعِظُونَ قَوۡمًا ٱللَّهُ مُهۡلِكُهُمۡ أَوۡ مُعَذِّبُهُمۡ عَذَابٗا شَدِيدٗاۖ قَالُواْ مَعۡذِرَةً إِلَىٰ رَبِّكُمۡ وَلَعَلَّهُمۡ يَتَّقُونَ ٤٦١
" KUMA A LOKACIN WA WATA AL'UMMA DAGA CIKINSU SUKA CE (ga masu yin wa'azi), DON MENENE KUKE YIN WA'AZI GA MUTANEN DA ALLAH ZAI HALAKAR DASU KO YAYI MUSU AZABA MAI TSANANI ! (masu wa'azin) SUKA CE , " UZURI MUKE NEMA WAJEN UBANGIJINKU WALA-ALLAH KO ZA SUYI TAQAWA (ta hanyar wa'azin namu). "
Haka suka cigaba da yin hani ba su fasa ba, su kuma 'yan ba ruwanmu na kallonsu suna cewa kun hada kansu da aiki.
Shine Allah (T) yace,
" فَلَمَّا نَسُواْ مَا ذُكِّرُواْ بِهِۦٓ أَنجَيۡنَا ٱلَّذِينَ يَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلسُّوٓءِ وَأَخَذۡنَا ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ بِعَذَابِۭ بَـِٔيسِۭ بِمَا كَانُواْ يَفۡسُقُونَ ." ٥٦١
" TO, A YAYIN DA SUKA MANTA DA ABINDA MUKE TUNATAR DASU A KANSA (na kamun kifi ranar asabar sai aka aiko da azaba a kansu) MUKA TSERATAR DA MASU YIN HANI DAGA (aikata wannan) MUMMUNAN AIKI (su kadai), KUMA MUKA KAMA WADANDA SU KAYI ZALUNCI DA AZABA MAI (matuqar) MUNI SAKAMAKON ABINDA SUKA KASANCE (suna aikatawa) NA FASIQANCI. "
(A'ARAF :164-165)
Yi nazari sosai dan'uwa, abinda Allah yace mana shine, da azabar tazo an tseratar da masu yin hani ne kadai, kuma aka halakar da azzalumai masu aikata abinda aka hane su.
Abinda wannan ke nuna mana shine, an raba al'ummar gida biyu ne, aka tseratar da masu yin hani kuma aka halakar da azzalumai.
A tunaninka ina 'yan ba ruwanmu suka shiga ? Cikin azzalumai ko cikin masu yin hani ?
IDAN KA SAMI KANKA CIKIN KASHI NA UKU KA FADA CIKIN AZZALUMAI.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08126385470)
23rd December, 2020/ 9th Jimada-Ulah, 1442.