-Imam Rida (AS) Yace: “Duk Wanda Ya Samu 'Dan uwa a tafarkin Allah to Ya Samu gida a Cikin Aljanna.”
-Imam Sadik (AS) Yace: “Mumini Dan uwan Mumini ne, Yadda Suke Kamar Jiki guda ne, idan Wani Sashe Ya yi Ciwo to Sauran Jiki zai ji radadi, ruhinsu Kuma daga ruhi guda ne:''
-Imam Ali (AS) Yana Cewa: “Duk Wanda Yaso Ka Saboda Wani abu, to idan abun Ya kare zai
Juya Maka baya.”
-Imam Ali (as) Yana Cewa: “Duk Wanda Sonsa ba Saboda Allah bane, to Kayi Hankali dashi, Saboda irin Wannan so da Kuma abota Babu Alkhairi a Cikinta.”
-Imam Ali (as) Yana Cewa, “Duk Wanda Yayi ‘Yan uwantaka Saboda Allah, to zai Samu ribarta, Wanda Kuma Yayi ‘Yan uwantaka Saboda l Duniya,to Zai yi Hasararta.”
-Imam Bakir (as) Yace: “Allah Ta’ala Yana da Wani gida a Cikin Aljanna ba Wanda Zai Shige shi Sai Wadannan ukkun:
(1) Wanda ya ziyarci Dan uwansa Mu'umini Saboda Allah.
(2) Wanda Ya Fifita Dan uwansa akansa Saboda Allah.
(3) Wanda Ya yi Hukunci akan Kansa da gaskiya.”
-Imam Sadik (as) Yana Cewa: “Lalle Mutum zai iya Fita domin Ya ziyarci Dan uwansa, amma Kafin Ya dawo zai Kasance duk an Gafarta Masa Zunubansa, an Kuma biya Masa bukatunsa na duniya da Kuma lahira.”
-Imam Sadik (as) Yana Cewa: “Duk Wanda Ya Ziyarci Dan uwansa Saboda Allah, Allah Ta’ala zai Ceto Wanda ka Ziyarta, Kuma ladarka tana gareni, Kuma baka da Wani Sakamako a Wajajena Face Aljanna.”
-Manzon Allah (S) Ya Kasance idan Ya Kwana ukku bai ga Wani ba daga Cikin Sahabbansa, to Ya kan Tambaya dangane dashi, in Ya ji an ce Yayi tafiya ne to sai Yayi Masa addu’a na Allah Ya dawo dashi lafiya. In Kuma bai da lafiya ne sai ya je Ya gaida shi. In Kuma Yana nan Kalau Sai Ya ziyarce Shi.”
-Manzon Allah (S) Yace: "Duk Muminin da Ya Ziyarci 'Dan uwansa Mumini Saboda Allah, to Allah zai gafarta Masa Zunubansa.